logo

HAUSA

Kamar Dai Kasar Amurka Ce Za Ta Kara Amfana Da Manufarta Ta Karfafa "Kawancen Demokradiyya" Da Take Dogaro Da Ita

2021-02-07 22:01:50 CRI

Kamar Dai Kasar Amurka Ce Za Ta Kara Amfana Da Manufarta Ta Karfafa "Kawancen Demokradiyya" Da Take Dogaro Da Ita_fororder_微信图片_20210207213430

Idan “moriya” ita ce muhimmiyar kalma ta tsohuwar gwamnatin Amurka, to a bayyane take ana iya cewa sabuwar gwamnatin Amurka ta sanya “ra’ayin martaba” a wani matsayi mafi muhimmanci.

Ko dai jawabin da shugaba Biden ya yi game da manufar diflomasiyya a kwanan nan a ma'aikatar harkokin waje ko kuma jerin matakan da tawagar diflomasiyyar Amurka ta dauka bayan hawan karagar mulki, dukkansu sun isar da wani muhimmin sako: kyautata dangantaka da kawayenta yana matsayin fifiko na ajandar gwamnatin Amurka ta yanzu, kuma wannan na nufin cimma wani burin gaggawa na sake gina tsarin "dimokiradiyya" a matsayin wata babbar manufa mafi daraja ta kulla kawance.

Amma ta yaya irin wannan kawancen ke iya janyo hankulan bangarorin da abun ya shafa?

Cikin sauri kasashen EU suka bayyana ra'ayoyinsu. A ranar 5 ga wata, shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta ce, duk da cewa Turai da Amurka suna da ra’ayin bai daya a fannoni da dama, amma har yanzu Turai na bukatar wata '' manufar kasar '' mai zaman kanta. A ranar 4 ga wata, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron shi ma ya nuna irin wannan ra’ayi, yana mai cewa, duk da cewa kungiyar EU da Amurka suna da akida daya, amma bai kamata su hada kai da Amurkar don nuna adawa da kasar Sin ba.

Gaskiya ne, a zamanin dunkulewar duniya baki daya, kasashe daban daban suna da alakar bai daya kan batun moriyarsu, kuma yaduwar annobar COVID-19 ta kara sanya duniya ta fahimci muhimmancin hadin kai. A hakika dai, hatta Biden da kansa ya jaddada bukatar hada kai tare da kasar Sin. Me ya sa wasu kasashe suka zabi tsayawa a bayan Amurka don yin gaba da kasar Sin, har ma suna lahanta moriyar kansu saboda kasar ta Amurka? (Mai fassara: Bilkisu Xin)