logo

HAUSA

An gudanar da bikin kidaya lokacin da ya rage na gudanar da gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu da ta nagasassu

2021-02-05 15:18:58 CRI

Daren jiya Alhamis, an yi bikin kidaya lokacin da ya rage, wato shekara 1, na gudanar da gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2022 a cibiyar ninkaya ta “Shuilifang” dake nan birnin Beijing. A wannan biki, a karon farko aka gabatar da wutar yula ta gasar mai suna “Feiyang”. Wannan wutar yula na dauke da ra’ayin da Sin take dauka wajen gudanar da wannan gasa da kuma al’adun kasar.

Masu sauraro, abokiyar aikinmu Amina Xu za ta hada mana da cikakken bayani.

Alamar wutar yula ta gasar wasannin Olympic a lokacin hunturu na kunshe da kuzari matuka, launinta shi ne azurfa da ja wanda ke alamta hadewar kankara da wuta. Kuma alamar wutar yula ta gasar wasannin Olympic a lokacin hunturu na nagasassu na kama da shi, amma an yi mata launin zirariya da azurfa, wanda ya bayyana ruhin wasannin nakasassu wato jarumta da alkawari da kara himma da kwazo da adalci.

Beijing ya zama birni na farko da zai karbi bakuncin gasanni irin wadannan biyu. Mai tsara wutar yula Li Jianye ya ce, ya tsara siffarta ne bisa siffar ganyen itace. Ya ce,

“Mun ga wani ganyen itace, sai tunani ya fado mana. Mun yi kirkire-kirkire matuka kan tsara wutar, inda siffarta ta yi kama da kirtani mai launi, kuma wutar na wasa a tsakiyar wadannan kirtani. Ban da wannan kuma, siffar wutar ba ta yi kama da kwallo ba kamar kullum, ta yi kama da wata dabbar Dragon dake shirin tashi sama.”

Wutar Yula ta “Feiyang” na kunshe da kimiya da fasaha na zamani matuka. Da farko an yi watsi da karfe, an yi amfani da kayan dake hade da Carbon fiber da Resin tare. Bayan wannan kuma, an yi kirkire-kirkire matuka kan fasahar samar da ita. Masani a wannan fanni kuma mataimakin manajan reshen Shanghai na kamfanin Sinopec Huang Xiangyu ya ce:

“Mun yi amfani da wata fasaha ta zamani, wanda ke iya sarrafa siffar kayayyakin Carbon fiber, ta yadda zai zama ko wane iri siffa da ake bukata. A wani bangare na daban kuma, mun yi amfani da wani kayan Resin dake iya daukar wuta ba tare da warkewa ba.”

Ban da wannan kuma, makamashi da wutar yula ta yi amfani da shi mai tsabta ne, abun da zata fitar ruwa ne kadai, ba za ta fitar da hayakin carbon-dioxid ba ko kadan. Babban injiniya na kamfanin CASC Han Zongjie ya ce, an yi nazari da kuma aikin gwaji sau da dama don bullo da wannan makamashi mai tsabta da kuma biyan bukata, wato iska mai karfi da saurinta ya kai kilomita 100 a ko wace awa, ba za ta kashe wutar yular ba.

Tun watan Afrilun shekarar 2020, aka fara sauraron jama’a kan shirin tsara wutar yula. Kwamiti mai shirya wannan gasa ta sami ayyuka 182 da aka gabatar mata daga duk fadin kasar Sin. Bayan an kimanta tare da nazari da kuma sauraron shawarwarin hukumar gasar Olympic ta kasa da kasa da ta nagasassu da kuma ra’ayin masana, sai aka tabbatar da shirin da ake aiwatarwa yanzu.

Shugaban kwalejin zane-zane na jami’ar Tsinghua Lu Xiaobo ya ce, shirin tsara wannan wutar yula na bayyana hadewar fasaha da kimiyya matuka. Mataimakin shugaban sashen kula da al’adu na hukumar shirya gasar Wang Xiangyu ya nuna cewa, kwamitin gudanarwa ta hukumar gasar Olympic ta kasa da kasa ta amince da “Feiyang” matuka, ya ce, “Feiyang” ta bayyana cewa, gasar wasannin Olympic wani dandali ne dake dunkule wasanni da al’adu da fasaha da kuma kimiyya, ba ma kawai al’adu ta gada ba, har ma ta yi kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha sosai. A cikin wannan biki da aka yi a wannan rana, shugaban hukumar wasannin Olympic na kasa da kasa Thomas Bach ya gayyaci hukumomin Olympic na kasashe da yankuna daban-dabana da su halarci wannan gaggarumin gasa da za a yi badi a birnin Beijing ta kafar bidiyo. (Amina Xu)