logo

HAUSA

Sin ta na cika alkawarin da ta dauka na tallafawa shirin COVAX

2021-02-04 20:17:28 CRI

Sin ta na cika alkawarin da ta dauka na tallafawa shirin COVAX_fororder_20210204-Sharhi-Saminu

Yayin da duniya ta shiga wani mataki na yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma kasashe daban daban ke ta hankoron samar da rigakafi ga al’ummun su, a wani mataki na gaggauta shawo kan annobar COVID-19, wadda ta zamewa duniya “kadangaren bakin tulu”, masana da masu fashin baki na ta jaddada muhimmancin baiwa juna goyon baya, da hadin gwiwa, domin yakar wannan cuta tare kuma cikin gaggawa.

Masana da dama na bayyana cewa, kawar da cutar a wasu yankuna, ba tare da la’akari da halin da wasu yankunan ke ciki game da ita ba, tamkar “kashe maciji ne ba tare da sare kansa ba”, wato dai “baya na iya haihuwa”.

Cikin jerin kasashen duniya da suka fara sarrafa alluran rigakafin cutar ta COVID-19 a cikin gida, kasar Sin ta zama “zakaran gwajin dafi” a fannin cika alkawarin da ta dauka tun tuni, na samar da rigakafin ga kasashe masu tasowa, karkashin shirin nan na COVAX, bisa kiran da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi.

A farkon wannan mako ne kasar Pakistan, ta samu kason farko na rigakafin da kasar Sin ta alkawarta tallafawa kasashe daban daban da shi. Inda tuni aka fara yiwa jami’an lafiya dake aiki a sahun gaba a yakin da kasar ke yi da cutar wannan rigakafi.

Baya ga Pakistan, Sin ta sha alwashin tallafawa karin kasashe masu tasowa 13 da wannan rigakafi a zagaye na farko, a kuma zagaye na biyu karin kasashe 38 za su ci gajiyar tallafin na Sin. Sin na fatan samar da rigakafi har miliyan 10 karkashin wannan kuduri.

Ko shakka ba bu, abun da wannan mataki ke nunawa shi ne, har kullum Sin na dagewa wajen cika alkawuran da ta dauka a matakai na yankuna, da na shiyya shiyya da ma na kasa da kasa.

Har ila yau Sin na da fatan ganin an rage gibin samar da alluran na rigakafi, tsakanin kasashe mawadata da masu tasowa, karkashin matakan da WHO ke dauka na cimma wannan buri.

Bugu da kari, matakin na Sin zai tabbatar da nasarar raba rigakafin gwargwadon bukata a dukkanin sassan duniya, zai kuma raya burin yaki da wannan annoba cikin hadin gwiwa, tare da goyon bayan manufar samar da tsarin kiwon lafiya na bai daya, ga dukkanin al’ummun duniya.

Yanzu haka dai sassa daban daban, na da fatan ganin sauran manyan kasashe su ma su yi koyi da kasar Sin, wajen marawa shirin COVAX na WHO baya, ta yadda za a kai ga shawo kan wannan cuta a dukkanin sassan duniya kuma a kan lokaci. (Saminu Alhassan)

Bello