logo

HAUSA

Riga kafin COVID-19 da kasar Sin ta samar na kara samun karbuwa a duniya

2021-02-03 19:08:22 CRI

A yayin da yawan masu harbuwa da cutar COVID-19 ya ragu cikin makonni uku a jere, a hannu guda kuma, hankalin al’ummar duniya na kara kwanciya, ganin yadda alluran riga kafin annobar da aka samar a sassa daban-daban na duniya ciki har da wadda kasar Sin ta samar, suke kara samun karbuwa a kasashen duniya.

Riga kafin COVID-19 da kasar Sin ta samar na kara samun karbuwa a duniya_fororder_20210203世界21005-Riga kafin COVID-hoto2

Koda yake a baya, hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadi kan yadda wasu kasashen yamma ke kokarin yin babakere kan alluran riga kafin, maimakon taimakawa kasashe marasa karfi, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. Kamar yadda kasar Sin ta yi alkawari tun farko cewa, da zarar ta kammala bincike, samarwa har ma aka fara amfani da riga kafin, to al’ummar duniya za ta ci gajiyarsa, musamman kasashe masu tasowa.

Yanzu haka, wasu kasashe kamar Pakistan, sun fara amfani da tallafin riga kafin da kasar Sin ta samar, inda ta samar mata da riga kafi dubu 500 kamar yadda ta yi alkawari.

Riga kafin COVID-19 da kasar Sin ta samar na kara samun karbuwa a duniya_fororder_20210203世界21005-Riga kafin COVID-hoto3

A halin yanzu an yiwa shugabannin wasu kasashe irinsu na Turkiya da Indonesia alluran riga kafin da kasar Sin ta samar, sannan wasu kasashen Turai irinsu Peru da Hungary har ma da Jamus, sun nuna sha’awarsu ta sayen riga kafin da kasar Sin ta samar, abin da ke kara nuna inganci da tsaron wannan riga kafi. Bayanai na nuna cewa, yanzu haka an yiwa sama da mutane miliyan 20 wannan riga kafi a kasar Sin. Ana kuma fatan kara yiwa daukacin jama’a riga kafin, bayan kammala shagulgulan bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)