logo

HAUSA

Da fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da sauyin shugabannin tsaro a Nijeriya

2021-02-02 18:21:21 CRI

Da fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da sauyin shugabannin tsaro a Nijeriya_fororder_微信图片_20210202154830

A makon da ya gabata ne shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya sauya shugabanni tsaron kasar da suka hada da Babban Hafsan Tsaro da Manyan Hafsoshin Sojin kasa da na sama da na ruwa, domin ci gaba da tunkarar matsalolin tsaron da kasar take fama da su.

Batun sauya manyan hafsoshin tsaron, zance ne da al’ummar kasar da dama suka sha yi, inda suka yi ta kira ga shugaban kasar da ya sauke tsoffin shugabannin da suka shafe shekaru 5 a kan mukamansu. A ganinsu, yin hakan shi zai shawo kan matsalolin tsaro dake ci gaba da kunno kai a kasar.

Jama’a za su kara sa ran cewa sabbin kwamandojin za su kawo canjin da ake fata, musamman kawo karshen ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram da aka shafe shekaru 10 ana fama a yankin arewa maso gabashin kasar, duba da cewa, suna da gogewa yayin da biyu daga cikinsu suka taba jagorantar ayyukan yaki da kungiyar a baya.

Sai dai, ba rikicin arewa maso gabashin kasar kadai ne a gabansu ba, akwai sauran miyagun laifuffuka dake wakana a kasar, kamar na satar mutane domin neman kudin fansa da ya zama ruwan dare da fashin teku da sace-sace da ma sauran ayyukan tsageru da kuma rikicin kabilanci.

Da fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da sauyin shugabannin tsaro a Nijeriya_fororder_微信图片_202102021548301

Babu wata al’umma da za ta samu ci gaba face tana zaune lafiya cikin kwanciyar hankali. Wadannan dai sabbin shugabannin tsaron, su ma mutane ne kamar wadanda suka gabacesu, don haka, ya kamata al’ummar kasar da suka yi ta kiraye-kirayen a saukesu, su kwan da sanin cewa, batun tsaro ya zarce wasu ‘yan tsirarun mutane.

Duk da cewa kamar yadda ake fata, wadannan manyan hafsoshi za su zo da na su sabon kuzari da salo da dabarun magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar, su ma jama’a ya kamata su sake daura damarar bada ta su gudunmuwa ta hanyar ba jami’an tsaro hadin kai da suke bukata da kiyaye ka’idoji da dokoki da kuma fallasa duk wani abu da ka iya tarnaki ga tsaron kasar, ba tare da la’akari da alakar da suke da shi ga masu kitsa matsalolin ba.

Su ma a nasu bangaren, ya kamata sabbin shugabannin su kwan da sanin irin yakini da fatan da ake da shi kan su. Ya kamata su dage, su tsaya tsayin daka wajen sauke nauyin dake wuyansu na tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a dukkan fadin kasar ba tare da nun fifiko ko yin watsi da wani bangare ba. Domin mutane da dama, kamar ‘yan gudun hijira da wadanda aka sace da wadanda aka raba da iyalansu, da ma daukacin al’ummar kasar, na ganinsu a matsayin maganin matsalarsu. (Faeza Mustapha)

Fa'iza