Alluran rigakafin COVID-19 da Sin ta samarwa ketare kyauta karo na farko sun isa Pakistan
2021-02-02 13:12:20 CRI
A safiyar ranar 1 ga wata, alluran rigakafin cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta samar wa kasashen ketare kyauta bisa mataki na farko sun isa Islamabad, fadar mulkin kasar Pakistan, gwamnatin kasar ta Pakistan ta nuna godiyarta ga gwamnatin kasar Sin, saboda alluran sun kawo haske gare ta yayin da take kokarin kandagarkin annobar.
Jiya Litinin ranar 1 ga wata da yamma, an mika alluran rigakafin cutar COVID-19 dubu 500 wanda gwamnatin kasar Sin ta samar kyauta ga gwamnatin kasar Pakistan a sansanin sojojin saman kasar ta Nurhan dake kusa da birnin Islamabad, fadar mulkin kasar, inda ministan harkokin wajen kasar Shah Mahmood Qureshi ya halarci bikin mikawa. Daga baya ya zanta da manema labarai na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 ga kasarsa cikin sauri a lokacin da kasar take fama da annobar, lamarin da ya nuna zumunci mai zurfa dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Pakistan, kuma a madadin gwamnatin Pakistan da al’ummun kasar, ya nuna babbar godiya ga kasar Sin, yana mai cewa, “Ina farin ciki matuka da samun allurar rigakafin cutar COVID-19 kyauta wanda kamfanin hada magunguna na Sinopharm na kasar Sin ya samar, lamarin ya sake shaida zumunci mai zurfi dake tsakanin kasashen Sin da Pakistan a ko da yaushe, har kullum muna goyon baya ga juna, musamman ma a lokacin da muke shan wahala.”
Qureshi, ya kuma nuna godiya ga kasar Sin saboda tura tawagar likitoci ga kasarsa yayin da suke kokarin dakile annobar, ya dauka cewa, fasahohin kandagarkin cutar COVID-19 na masana likitanci na kasar Sin sun taimaka matuka kan aikin dakile annobar a kasar ta Pakistan, yana mai cewa, “Tawagar masana kiwon lafiya ta rundunar sojojin yantar da jama’ar kasar Sin da sauran likitocin kasar Sin sun zo Pakistan domin taimakon mu, haka kuma sun horas da likitocinmu, a nan ina son nuna babbar godiya saboda kokarin da kasar Sin take yi domin taimaka mana.”
Kana gwamnatin kasar Pakistan ta bayyana cewa, za a yiwa ma’aikatan kiwon lafiyar dake aiki a asibitocin kasar alluran rigakafin da kasar Sin ta samar, darektan zartaswa na cibiyar nazarin kiwon lafiya ta kasar Pakistan Aamer Ikran ya bayyana yayin da yake zantawa da manema labaranmu cewa, za a fara aikin yin alluran tun daga gobe ranar 3 ga wata, ya ce, “Mun godewa gwamnatin kasar Sin kwarai da gaske saboda ta samar mana alluran rigakafin cutar COVID-19 kyauta, mun lura cewa, alluran rigakafin da kamfanin hada magunguna na Sinopharm na kasar Sin ya samar suna da inganci, zamu fara aikin yin alluran daga gobe ranar 3 ga wata a birnin Islamabad, daga baya zamu yi jigilar alluran zuwa sauran sassan kasar.”
A halin da ake ciki yanzu, hukumar kula da magunguna ta Pakistan ta riga ta amince da amfanin allurar Sinopharm na kasar Sin a matakin gaggawa. A sa’i daya kuma, an kusan kammala aikin gwajin allurar rigakafin COVID-19 da kamfanin CanSino na kasar Sin ya samar a jikin mutane a mataki na uku a Pakistan.
A madadin gwamnatin kasar Sin, jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Pakistan Nong rong ya mika alluran rigakafin ga gwamnatin kasar Pakistan, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta san babbar bukatar allurar rigakafin COVID-19 a fadin duniya, a don haka tana sanya kokari domin samar da karin tallafi da goyon baya a bangaren, kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Pakistan a bangaren samar da allurar rigakafin zai amfanawa al’ummun duniya, yana mai cewa, “Ina farin cikin sanar da cewa, Pakistan ce kasa ta farko da ta samu alluran rigakafin cutar COVID-19 wanda gwamnatin kasar Sin ta samar wa kasashen ketare kyauta, kowa ya sani, Pakistan aminiyar kasar Sin ce, inda ake gudanar da hadin gwiwa wajen samar da allurar rigakafin, a nan ina son nuna godiya ga gwamnatin Pakistan saboda amincewa da yin amfani da allurar Sinopharm na kasar Sin a matakin gaggawa, da goyon bayan da take bayarwa ga kamfanin CanSino na kasar Sin yayin da yake gudanar da gwajin allurar a jikin mutane a mataki na uku, ina fatan kasashen biyu zasu kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda al’ummun kasashen duniya za su ci gajiya.”(Jamila)