logo

HAUSA

Dalibar dake sha’awar kiwon tumaki

2021-02-02 09:08:40 CRI

Wang Meiling, wacce ke zaune a garin Hedao na gundumar Huan dake birnin Qingyang na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin, ta kammala karatu a kwalejin koyar da sana’o’i da fasaha ta Gansu a shekarar 2012. Wannan mace da ta koyi fasahar nazarin masana’antu da gwaji, ba ta taba tunani wai aikinta zai shafi tumaki ba. Wang Meiling ta gaya mana cewa,

"Na ji an ce, dalibai da yawa da suka kammala karatunsu a jami’a ko kwaleji sun dawo garinmu don fara kasuwancinsu na kiwon tumaki, don haka ni ma ina so in dawo don gudanar da irin aiki, da nufin ganin ko zan iya ko ba zan iya ba."

Dalibar dake sha’awar kiwon tumaki_fororder_王美玲

Gundumar Huan yanki ne mai matukar talauci, yana cikin manyan tsaunuka, kuma akwai ramuka masu zurfi, kana kasar yankin ba ta da amfani. Amma albarkatun halittu na musamman na ba mazauna yankin damar rungumar kiwon tumaki da ciyawa tun fil azal. A cikin 'yan shekarun nan, bisa la'akari da fa'idodin albarkatu, yankin yana ta kokarin bunkasa masana'antar tumaki, wanda ba wai kawai ya taimakawa jama’ar wurin kawar da talauci da kuma samun wadata ba, har ma an bude wata kyakkyawar hanya ga daliban da suka kammala karatu a jami’a ko kwaleji don komawa garinsu don raya sana’a. A shekarar 2019, gundumar Huan ta kafa kungiyar raya sana’ar kiwon tumaki ta dalibai, ta hakan aka cike gibin dake kasancewa na neman kwararru don bunkasa masana'antu, a sa’i daya kuma, aka gina wani dandamali mai kyau ga matasa don raya sana’a.

Rage kudin haya, ba da rancen kudi ba tare da biyan ruwa ba, da kuma samar da tallafi wajen samun aikin yi a cikin shekaru 3 ... wato Jerin manufofin ba da taimako da gwamnatin wurin ta kaddamar, sun burge Wang Meiling sosai. Ta ce,

“Da na ga irin bayanan daukar ma'aikata da aka bayar a yanar gizo a farkon rabin shekarar da ta gabata, sai na yi matukar farin ciki sosai.”

Tare da damuwa, Wang Meiling ta isa sansanin kiwon dabbobi na Dongyuan dake gundumar ta Huan. Da ma ta yi fatan yin tambaya tukuna don kara fahimtar hakikanin halin da ake ciki game da shiga kungiyar ta raya sana’ar kiwon tumaki, amma bayan yin tambayar sai ta sanya hannu don shiga kungiyar. Ta ce,

“An kawar da damuwa ta, an gaya min cewa, bayan an shiga kungiyar raya sana’ar kiwon tumaki ta dalibai, gwamnati za ta ba da kudin horo, dalibai masu yawa a nan sun soma ayyukansu bayan samun horo, kamar yadda nake, akwai wadanda ba su taba sanin sana’ar ba da yawa.”

Sanye tufafin aiki tare da daukar abincin raguna, Wang Meiling ta tuna yadda take farin ciki a karon farko da ta shiga cikin garken tumakin. Ta ce,

"Bayan kwanaki 30 da ba mu horo, a karshe zan iya aiwatar da aikin. Ina matukar farin ciki a lokacin."

Dalibar dake sha’awar kiwon tumaki_fororder_src=http___p8.itc.cn_q_70_images03_20210118_ecf4d5f7a2184cb0a029e69d3069cca6.jpeg&refer=http___p8.itc

Amma, lokacin da ta shiga cikin garken tumakin, warin da ta ji nan da nan ya kashe sha'awarta.

Wang Meiling ta gaya mana cewa,

"Da farko, warin ya dameni sosai, amma daga baya sai na saba da shi ."

Ta ce, tumaki masu kyau sun sanya ta manta da warin garken tumaki cikin sauri, a ganin ta, sai ta tsaya kan rashin jin tsoron wahala da wari, ta fahimci yadda zaman rayuwar tumaki suke a yau da kullun, sannan za ta iya zama kwararriyar mai kiwo.

Bayan ta yi niyya, Wang Meiling ta kan kwashe yini guda cikin garken tumaki, tana koyon ilmi iri-iri da suka shafi kiwon tumaki, da rigakafin annoba.

Yanzu dai, wa’adin samun horo ya kare, Wang Meiling ta samu nasarar zama ainihin ma'aikaciya, ta soma aiki a sansanin kiwon dabbobi na Dongyuan na gundumar Huan.

Wang Meiling ta ce,

"A duk lokacin da na ga tunkiya tana haihuwa, ina matukar farin ciki. Kula da su daidai yake da yadda ake kula da yara." “Ina kulawa da tumaki kusan 3,000. A wannan lokacin, ganin karuwar yawan tumakin, na sani jin dadi sosai a cikin zuciyata.”

Yanzu haka an daga matsayin Wang Meiling daga mai kiwo zuwa ga mai fasaha. Ba kawai ta bai wa kowane tunkiya alamar kunne don gano halin lafiyarsu da shekarunsu na haihuwa ba, har ma ta zama "tsohuwar abokiya" ta wadannan tumakin. Ta ce,

“Da farko na ji cewa, wadannan tumaki kamarsu daya ne, amma bayan lokaci mai tsawo, ina iya bambanta su daya bayan daya.”

Shugaban kungiyar raya sana’ar kiwon tumaki ta dalibai ta gundumar Huan Ji Yongfeng ya bayyana cewa,

“Gundumar Huan babbar gunduma ce ta kiwon tumaki a lardin Gansu. Naman tumaki masu inganci da tumaki irin na Hu da na Tan suke wakilta, suna samun karbuwa sosai.”

Dalibar dake sha’awar kiwon tumaki_fororder_Wang

A ganinsa, a cikin 'yan shekarun nan, bisa ci gaba da sauyawar tsarin inganta sana’ar kiwon tumaki ta gundumarsu, horar da kwararru a fannin ya zama wata sabuwar matsalar da ke hana ci gaban sana’ar. Ya ce, “Kafuwar kungiyar raya sana’ar kiwon tumaki ta dalibai, wani bincike mai kyau ne da aka yi, ba kawai ya kafa wani dandamali na horar da kwararru ba, har ma ya samar da wata hanya ga fitar da kwarewa.”

Ji Yongfeng ya bayyana cewa, dalibai suna da karfin karbar sabbin abubuwa da kuma hangen nesa, hakan ya sa aka iya shigar da sabbin jini don ci gaban sana’ar. A waje guda kuma, a karkashin jagoranci da goyon bayan gwamnati, ana iya kara wa daliban kwarin gwiwar raya sana’a, kana kuma ana iya horar da kwararru masu yawa don su taka rawar jagorantar bunkasuwar sana’ar ta kiwon tumaki.

Ya zuwa yanzu, yawan tumakin da aka kiwata a gundumar Huan sun zarce miliyan 2.1, kuma dalibai kusan 500 sun ba da hidima ga manyan sansanonin kiwon dabobbi da kungiyoyin hadin gwiwa na wurin, kuma suna daukar alhakin ba da jagoranci ga masana’antun dake kauyuka sama da 200.

Wang Meling ta ce,

“Da farko dai zan yi kokarin samun ilmin fasaha sosai, daga baya zan kwada cimma buri na, wato zan samar da wata kungiyar hadin kai ta kauye, don taimakawa mutane masu yawa samun wadata ta hanyar kiwon tumaki.”

Wang Meiling ta kuma cewa, ko da yake kasancewarta "mai kiwo" ya zama abun dariya wajen wasu, suna cewa tana "kamshi sosai", a ganinta, sai ta hanyar "jikewa’’ a cikin garken tumaki ne kadai za ta iya ganin cikar burinta.