logo

HAUSA

Wane albishir kamfanonin Sin ke yiwa duniya game da samun rigakafi?

2021-02-01 18:06:09 CRI

Wane albishir kamfanonin Sin ke yiwa duniya game da samun rigakafi?_fororder_微信图片_20210201154254

Masu salon magana na cewa “Wani kaya sai amale.” Yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar barazanar karuwar masu kamuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19, baki daya hankalin duniya ya karkata kan yadda za a samu wadatar alluran riga-kafin annobar. Masana sun yi ittifaki cewa babu wata sahihiyar hanyar da za ta bayar da cikakkiyar damar samun kashe kaifin annobar COVID-19 sama da yin amfani da riga-kafin cutar domin kashe tasirinta wacce ta zamewa duniya kadangaren bakin tulu. A yanzu haka, an fara samun riga-kafin cutar ta COVID-19 daga wasu kamfanonin kasa da kasa, sai dai babbar matsalar ita ce yadda wasu kasashen duniya masu wadata suke kokarin yin babakere wajen sayewa alluran riga-kafin cutar duk kuwa da irin kiraye-kirayen da MDD da hukumar lafiya ta duniya WHO da sauran kungiyoyin kasa da kasa ke yi na neman a tabbatar da raba daidai a tsarin mallakar riga-kafin cutar. To sai dai ba dukka aka taru aka zama daya ba, yayin da wasu kasashe masu sukuni suke ta kokarin gina kansu da fifita bukatun al’ummarsu sama da sauran kasashe marasa galihu, a nata bangaren, kasar Sin ta sha nanata matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya dake da burin hadin gwiwa da sauran kasashe masu karamin karfi domin taimaka musu don a gudu tare a tsira tare. Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sanya wasu manyan kamfanonin hada magunguna na kasar Sin suka dukufa wajen samar da riga kafin cutar domin wadata duniya da isassun riga-kafin annobar wacce ta gallabi duniya. Wani babban albishir da ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin MOST ta fitar a farkon wannan mako an bayyana cewa, a yanzu haka jimillar kamfanonin kasar Sin bakwai dake aikin samar da riga-kafin annobar COVID-19 sun shiga zagaye na uku na gwajin alluran riga-kafin. Kawo yanzu, kasar Sin tana da kamfanoni 16 dake aikin samar da riga-kafin annobar COVID-19 inda suke ci gaba da gudanar da gwajin alluran, Wu Yuanbin, shi ne darakta janar na ma’aikatar bunkasa kimiyya da fasaha na kasar Sin, ya bayyana a yayin wani taron da aka gudanar a kwanan nan game da binciken dake shafar gwaje-gwajen jini. Riga-kafin wanda ba a kai ga kammala shi ba, wanda cibiyar nazarin tsirrai ta Beijing ke shirin samarwa, yana karkashin babban kamfanin kimiyya na kasar Sin CNBG, dake hadin gwiwa da kamfanin hada magunguna na SinoPharm na kasar, wanda shi ne na farko da ya samu izinin shiga kasuwanni bisa sahhalewar hukumar kula da magunguna ta kasar Sin a watan da ya gabata. Ko shakka babu, wannan wani labari ne mai faranta rai kasancewar bayanai sun nuna cewa sakamakon gwajin da aka samu a zagaye na uku ya nuna ingancin riga-kafin na COVID-19 wanda kamfannin Sin suke cigaba da kokarin samarwa ya kai kashi 79.34 bisa 100. Dama dai an ce “Jumma’a mai kyau tun daga Laraba ake gane ta.” (Ahmad Fagam)

Bello