logo

HAUSA

Ingantaccen tsarin sufuri na baiwa Sinawa damar sake saduwa da danginsu lafiya

2021-01-31 21:03:25 CRI

Ingantaccen tsarin sufuri na baiwa Sinawa damar sake saduwa da danginsu lafiya_fororder_0131-sharhi-Bello

12 ga watan Fabrairun bana bikin bazara ne na kasar Sin. Bikin bazara shi ne farkon shekara da aka kayyade bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma shine biki mafi muhimmanci a zukatan Sinawa. Bisa al'ada, dole ne dukkan mutane su hadu da dangoginsu a wannan lokacin, kuma su yi bikin murnar sabuwar shekara cikin farin ciki tare. Saboda haka, kewayowar bikin bazara na kowace shekara shi ne lokacin da ake samun kwararar mafi yawan jama’a a nan kasar Sin. Kafin da bayan bikin bazara na shekarar 2015, kasar Sin ta samu zirga-zirgar jama'a biliyan 3.7 (ta jiragen kasa, motoci, jiragen sama, jiragen ruwa da sauran hanyoyin sufuri), wanda yayi daidai da yawan al’ummun nahiyoyin Afirka, Turai, Amurka, da Oceania baki daya.

Sai dai, yayin bikin bazara na wannan shekarar, ba za mu ga motsin mutane da yawa ba, saboda matakan hana bazuwar COVID-19 ya sa Sinawa kara yin taka tsan-tsan. Hukuma mai kula da layin dogo ta kasar Sin ta fitar da bayanan kwararar fasinjojin jirgin kasa na baya-bayan nan, wanda ya nuna cewa a cikin kwanaki uku na ranakun 28, 29, da 30 na Janairu, an samu kwashe fasinjoji miliyan 3.08, miliyan 2.83 da miliyan 2.96, bi da bi, kusan kashi daya bisa hudu na makamancin lokaci a bara. A bayyane yake, kiran da aka yiwa mutanen kasar na "ku zauna inda kuke a lokacin bikin bazara" ya sami goyon baya sosai daga jama'a.

Ko da yake, yawan fasinjojin ya ragu, matakan hana yaduwar COVID-19 ba su sassauta ba kwata-kwata. Farawa daga 28 ga Janairu, ana bukatar fasinjoji su yi tafiye tafiye tare da takardun shaidar gwajin kwayar COVID-19. Bugu da kari, mutanen da ke bukatar yin tafiya ta jirgin kasa kai tsaye suna sayen tikiti a wayoyinsu na salula, kuma kai tsaye suna shiga tashar da katin shaida na ID don takaita haduwar da bata zama wajibi ba. Ana bukatar shiga da fita tashar tare da karbar gwajin zafin jiki da bincika wata lambar dake cikin wayar hannu don yin rijistar motsi na mutum, ta yadda ake iya tabbatar da cewa mutanen da ke da alamun zazzabi za a iya ganowa da kebe su cikin sauri, kuma sauran mutanen da suka yi cudanya da su za a iya kebe su, da sanya musu ido cikin lokaci.

A cikin garin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar Sin, sashen kula da zirga-zirgar ababen hawa ya dauki matakin kashe kwayoyin cutar a cikin motocin bas dake shiga da kuma fita daga garin, ana kuma auna yanayin zafin jiki na dukkan fasinjoji, da yin rajistar wuraren da suka bi, da basu marufin baki da hanci, da kuma nesanta kujerunsu. A tashar jirgin kasa ta Beijing, babban birnin kasar, jami'an 'yan sanda 114 na bakin aiki cikin awanni 24 na rana domin tabbatar da ana iya daidaita wasu al’amuran gaggawa da suka shafi tsaron jama'a ko kuma annobar COVID-19 nan take. A tashar motar bas din da ke kudancin garin Guangzhou, ma’aikatan suna taimakawa fasinjoji masu yawan shekaru da ba su da wayoyi masu kyau ko kuma ba su fahimci yadda ake sarrafa wayoyin salula ba, wajen kammala rajistar da ake bukata don rigakafin cutar COVID-19. Duk wadannan matakan ana daukarsu ne don tabbatar da lafiyar fasinjoji da kuma samun damar shawo kan hadarin yaduwar cutar COVID-19.

Kashegari jiya, a garin Haikou dake kudancin China, wani matafiyi ya fada wa manema labarai cewa, "Hankalina ya kwanta ganin yadda matakan kandagarkin cutar suke da tsauri." Tabbas, kimantawar da Sinawa suka yi game da matakan da kasar ta dauka ta fuskar dakile cutar COVID-19 ita ce "zama hankali kwance". A kasar Sin, mutane sun ga yadda dukkan sassan gwamnati da kungiyoyi daban daban aka dunkule waje guda don gudanar da ayyukan dakile cutar COVID-19 tare domin tabbatar da ganowa da kuma hana yaduwar cutar a kan lokaci. Kana bisa kokarin shawo kan annobar, ayyukan samar da kayayyaki da zaman rayuwar jama’a sun daidaita.

A halin yanzu, cutar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a duniya, amma Sinawa sun yi iya kokarinsu don ganin sun samu damar yin tafiye-tafiye ta jirgin kasa, da komawa gida hutu, da sake haduwa da danginsu yadda suke bukata. Sinawa sun fahimci irin kokarin da suka yi kafin a cimma wannan nasarar. (Bello Wang)

Bello