logo

HAUSA

Sharhi: Kama bera a shagon sai da kayayyakin fadi-ka-mutu

2021-01-29 19:05:40 CRI

Sharhi: Kama bera a shagon sai da kayayyakin fadi-ka-mutu_fororder_微信图片_20210129180659

A ranar 27 ga wata, a gun taron manema labarai da gwamnatin birnin Shanghai ta kira, magajin garin birnin Mr.Gong Zheng ya bayyana cewa, an shawo kan yaduwar cutar Covid-19 a birnin.

Tun bayan da aka gano bullar cutar a ranar 20 ga wata, kawo yanzu, gaba daya an gano masu cutar 16 a birnin, kuma yadda aka dakile yaduwar cutar a wannan karo ya samu yabo sosai daga al’ummar birnin da ma sauran sassa daban daban, a sakamakon yadda aka nuna ra’ayin “sanya jama’a a gaban kome” a yayin daukar matakan kandagarkin cutar.

Kamar dai yadda Dr.Zhang Wenhong, shugaban sashen kula da cututtuka masu yaduwa na asibitin Huashan karkashin jami’ar Fudan na birnin Shanghai, wanda kuma shi ne shugaban tawagar masanan lafiya ta birnin ya bayyana cewa, tamkar “kama bera a shagon sai da kayayyakin fadi-ka-mutu ne” ake daukar matakan kandagarkin cutar a birnin Shanghai a kullum, wato ana son kama bera amma ba tare da lalata kayayyakin fadi-ka-mutu ba da ke cikin shagon ba, ma’ana ba a son haifar da tasiri sosai ga rayuwar al’umma a yayin daukar matakan kandagarkin.

Bayan gano bullar cutar a wannan karo, ba a dauki matakan kulle a birnin ba, kuma ba a gudanar da gwajin cutar da ya shafi gaba dayan mazauna birnin ba, a maimakon haka, an amince da wadanda za a killace su su je wajen killacewa tare da irin dabbobin da suke kiwo a gida kamar karnuka da kyanwa, baya ga haka, a bayanan da aka samar wa al’umma dangane da yanayin yaduwar cutar, an bayyana sassan da masu cutar suka taba zuwa ne kawai ba tare da ambaton jinsinsu da shekarunsu da dai sauran bayanan da suka shafi masu cutar ba.

Bayan gano bullar cutar a birnin, nan da nan aka fara aiki da tsarin ko da kwana, kuma yadda ma’aikatan cibiyar shawo kan yaduwar cututtuka suka suka hazarta binciko yanayin yaduwar cutar ba dare ba rana, ya sa cikin sauri ne aka tabbatar da wadanda suke dauke da cutar da wadanda suka taba yin mu’amala da su kai tsaye ko ba kai tsaye ba da kuma sassan da suka taba zuwa ta hanyar kimiyya, tare da killace su. Matakin da ya sa ba a kai ga daukar matakan kulle ko kuma gudanar da gwajin cutar a kan dukkanin mazauna birnin ba, wanda kuma ya saukaka tasirin da bullar cutar ta haifar ga ayyukan jama’a da rayuwarsu.

Baya ga haka, yadda aka bayyana wa al’umma sassan da masu cutar suka taba zuwa amma ba tare da ambaton bayanansu ba, ya kare sirrin masu cutar, lamarin da kuma ya bayyana manufar mutunta masu cutar, tare kuma da fahimtar da al’umma kan cewa, cutar ce abokin gabanmu a maimakon masu cutar.

Bayan da aka gano mai cutar a wata unguwar birnin kuma, an kaurar da mazauna unguwar cikin wani otel don killace su, kuma an yarda su je wurin killacewa tare da dabbobin da suke kiwo a gida kamar karnuka da kyanwa, don sassauta damuwarsu.

A hakika, yadda aka “kama bera a shagon sai da kayayyakin fadi-ka-mutu” a birnin Shanghai, ya faru ne bisa tushen kwarewar da aka samu a kasar Sin ta fannin dakile cutar bayan da ta shafe samar da shekara guda tana yakarta, haka kuma sabo da manufar “mai da jama’a a gaban kome” da aka saka a zuci a lokacin daukar matakan kandagarki.(Lubabatu)