logo

HAUSA

An cimma burin samar da ruwan sha mai inganci a karkarar kasar Sin

2021-01-28 14:18:09 CRI

An cimma burin samar da ruwan sha mai inganci a karkarar kasar Sin_fororder_7e3e29af59804348be8e6ebdfc78fe70_th

Samun ruwan sha mai inganci matsala ce da ta dade tana damun wasu sassan karkara na kasar Sin. Amma yanzu, an samu gaggarumin ci gaba ta wannan fanni, duba da cewa an warware matsalar daga dukkan fannoni ga al’ummar da ke fama da talauci a kasar Sin, sa’an nan, an daidaita matsalar samun ruwan sha mai gishiri a karkarar kasar, matakin da ya sa al’ummar kasar suka ga bayan matsalar karancin samun ruwa ko samun ruwan sha mai gishiri da suka dade suka fuskanta.

Kauyen Ucturfan keybulun da ke gundumar Yutian ta jihar Xinjiang yana arewacin tsaunin Kunlun, kuma mazauna kauyen sun dogara ne ga diban ruwa daga koguna da rafukan da suka ratsa wurin, sai dai ruwan ba shi da inganci sosai. Elican Hikim, wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa, “A baya, mu kan hau doki mu je wurin da ke da tazarar wasu kilomitoci daga kauyenmu don diban ruwa, amma akwai laka da kuma tsutsa a cikin ruwan, dole sai mun tace shi kafin mu sha.”

A shekarar 2018, an fara aiwatar da aikin samar da ruwan sha maiinganci a kauyen, aikin da ya daidaita matsalar samun ruwan sha mai inganci da mazauna kauyen 419 suka fuskanta. Yanzu haka, magidantan kauyen suna samun ruwan sha mai inganci, kuma malam Elican Hikim ya ce,“Yanzu muna shan ruwan famfo mai inganci, kuma cikin sauki muke samun ruwan sha.”

Kudancin jihar Xinjiang ya kasance ragowar sassan da al’ummar karkara masu fama da talauci ke fuskantar matsalar samun ruwan sha mai inganci a kasar Sin. A game da wannan, ma’aikatar ruwa ta kasar Sin ta tsara jadawalin aiki a gundumomi daban daban na kasar, musamman ma sassan da ke fama da talauci. Zhang Dunqiang, mataimakin shugaban sashen kula da samar da ruwa a kauyuka na ma’aikatar ruwa ta kasar Sin ya bayyana cewa,“Mun aiwatar da ayyuka na samar da ruwa mai inganci. A yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13, ma’aikatar ruwa ta hada gwiwa da hukumar kula da raya kasa da yin gyare-gyare da ma ma’aikatar kudi, kuma gaba daya gwamnati ta ware kudin Sin yuan biliyan 29.6 don tallafawa wannan aiki, baya ga kuma jarin da aka zuba daga sauran sassa na raya kauyuka, gaba daya an zuba jarin da ya kai yuan biliyan 209.3, matakin da ya sa kaimin aiwatar da ayyuka a sassa daban daban.”

A sabo da haka, bayan da aka fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13 a shekarar 2016, an aiwatar da ayyukan samar da ruwan sha mai inganci sama da 400 a kauyukan jihar Xinjiang, matakin da ya kawo karshen yanayin da sassan kudancin jihar suka samu kansu a ciki na dogara ga ruwan kogi a lokacin zafi, da kuma ruwan kankara a lokacin hunturu, kuma sama da kaso 90% na kauyukan jihar na samun ruwan famfo.

Ya zuwa karshen shekarar 2020 kuma, an daidaita matsalar samun ruwan sha mai inganci da al’ummar kasar miliyan 17.1 da ke fama da talauci suka fuskanta.

Malam Li Gang, wanda ya fito daga kauyen Lijiaqu da ke birnin Tianshui na lardin Gansu na kasar Sin, ya ce abin da ya fi faranta masa rai a shekarar 2020 shi ne ruwa ya fara zaki. Ya ce, a baya, sai an dafa ruwan, a kan samu nau’in farin gishiri a ciki, wanda in an dandana shi akwai daci. Amma yanzu, ruwan famfo da ake samarwa ba shi da matsalar. Yana mai cewa,“Yanzu ruwan ba shi da gishiri, kuma yana da inganci, muna iya gano hakan daga ruwan da muka dafa, wanda a baya mu kan samu tarin gishiri, amma yanzu ya ragu.”

Ruwan gishiri matsala ce da take damun wasu sassan lardin Gansu. Amma bayan da aka gudanar da ayyukan gyaran ruwan wurin, ya zuwa karshen shekarar 2020, an kammala aikin gyaran ruwan gishiri a gundumomi 31 na lardin, matakin da ya yi amfani ga al’umma dubu 395.   (Lubabatu)