logo

HAUSA

Sin ta samar da dabarun kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya

2021-01-28 19:07:04 CRI

Sin ta samar da dabarun kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya_fororder_2

Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi na musamman a yayin taron “Jadawalin Davos” na dandalin tattalin arzikin duniya ta kafar bidiyo, inda ya yi cikakken bayani kan ka’idar gudanar da harkokin duniya ta hanyar aiwatar da manufar cudanyar kasa da kasa, lamarin da ya jawo hankalin al’ummun fadin duniya matuka.

Jaridar Russian Gazette ta bayyana cewa, a cikin jawabinsa, shugaba Xi ya gabatar da ra’ayin Davos kan tsarin kasa da kasa bayan ganin bayan annobar COVID-19.

An lura cewa, dalilin da ya sa duniyarmu take fama da tangarda, shi ne yadda wasu kasashen yamma suka mayar da moriyar kashin kansu a gaban moriyar jama’ar kasashen duniya, haka kuma suna aiwatar da manufofin bangaranci da ba da kariya, duk wadannan sun sa daukacin kasashen duniya fama da kalubalen rikici. Kan wannan batu, shugaba Xi ya yi gardadi cewa, idan har kasashen duniya ba sa martaba ka’idojin da aka tsara wadanda suka amince daga duk fannoni, to lamarin zai harfar da babbar masifa ga bil Adama.

Sin ta samar da dabarun kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya_fororder_3

Game da yadda za a daidaita matsalar gibin dake tsakanin kasashe masu ci gaba da kasashe masu ttasowa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya kamata kasashen duniya su ba da cikakken goyon baya ga ci gaban kasashe masu tasowa, domin tabbatar da hakkinsu na samun ci gaba, a sa’i daya kuma, al’ummun kasashe daban daban za su ci gajiyar sakamakon ci gaban duniya tare. Tsokacinsa ya nuna cewa, shugaban kolin kasar Sin ya yi tunani mai zurfi kan muradun ci gaban duniya.

Hakika a ko da yaushe kasar Sin tana mai da hankali kan nuna adalci, haka kuma shugaba Xi ya gabatar da wasu shawarwari, alal misali, ingiza kwaskwarima kan tsarin hukumar cinikayya ta duniya da tsarin kudin kasa da kasa, kana ya yi kira a tabbatar da ajandar dauwamammen ci gaban MDD nan da shekarar 2030, kana ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, matakan da kasar Sin ta dauka sun shaida cewa, burin kasar Sin shi ne samun ci gaba tare, ba ma kawai tana da yunkurin samun wadata a cikin kasarta ba, har ma tana yin kokarin samar da wadata ga al’ummun sauran kasashe.

Amma akwai bukatar karin lokaci yayin da ake kokarin daidaita sabanin dake tsakanin kasa da kasa, muddin daukacin kasashen duniya sun nace kan manufar cudanyar kasa da kasa, da yin shawarwari domin cimma matsaya guda, to, za a kara kyautata tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa yadda ya kamata.(Jamila)