logo

HAUSA

Sinawa Na Gaf Da Fara Tafiye Tafiye Gabanin Bikin Bazara Bisa Ka’idojin Kandagarkin Cutar COVID-19

2021-01-28 18:30:41 CRI

Sinawa Na Gaf Da Fara Tafiye Tafiye Gabanin Bikin Bazara Bisa Ka’idojin Kandagarkin Cutar COVID-19_fororder_0128-2

Sinawa Na Gaf Da Fara Tafiye Tafiye Gabanin Bikin Bazara Bisa Ka’idojin Kandagarkin Cutar COVID-19_fororder_0128-1

Tun daga yau Alhamis ne ake sa ran Sinawa za su fara tafiye tafiye na komawa gida domin saduwa da iyalai, gabanin bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta kasar ta shekarar 2021.

Duk da kasancewar wannan biki mafi girma cikin jerin bukukuwan gargajiyar kasar, wanda a duk shekara idan ya zagayo, Sinawa ke tururawar komawa gida domin haduwa da iyali, a bana ana hasashen miliyoyin Sinawa za su yi hakuri da tafiye tafiye, domin kaucewa kara barkewar annobar COVID-19 da kasar ta sha fama da ita a bara.

Alkaluman kididdiga daga ma’aikatar sufurin Sin sun nuna cewa, cikin kwanaki 40 da ake shafewa ana tafiye tafiye masu nasaba da wannan biki, a bana ana hasashen samun zirga zirgar fasinjoji kusan biliyan 1.7, karuwar kaso 10 bisa dari a shekara, ko da yake wannan adadi zai yi kasa da kaso 40 bisa dari, idan an danganta da tafiye tafiyan da aka gudanar a makamancin lokaci a shekarar 2019.

Kaza lika domin dakile yaduwar wannan annoba, mahukuntan Sin sun fitar da wani tsari na takaita taruwar jama’a wuri guda, da baiwa al’umma shawarar hakuri da tafiye tafiye tare da fatan al’umma za su zauna wuri daya a lokutan bikin na bazara.

Karin han haka, wajibi ne fasinjoji su sanya takunkumin baki da hanci a lokacin da suke cikin ababen hawa, kana za a rika duba yanayin lafiyar jiki ta manhajar da aka tanada, a hannu guda ana shawartar matafiyan da su kaucewa ciye ciyen abinci a cikin ababen hawa.

A bana bikin bazara ya fado ne ran 12 ga watan Fabarairu, bikin da shi ne mafi haifar da zirga zirgar al’umma da ta fi ko wacce yawa a fadin duniya. Duk da muhimmancin wannan biki ga Sinawa, abun lura shi ne yadda miliyoyin su za su hakura da yin cikakken sa tare da iyalan su, domin kare lafiya da rayuwan su da na ‘yan uwa, kamar dai yadda Bahaushe kan ce “Zama lafiya ya fi zama dan sarki”.

A iya cewa, sadaukarwa irin wannan, wadda ta kunshi hakura da yin bukukuwa yada aka saba, da ci gaba da bin matakan kandagarki, da sauran ka’idojin tafiye tafiye da Sinawa ke bi, su ne suka zamewa kasar ginshikin kaiwa ga nasarar dakile yaduwar annobar COVID-19.

Hakan tamkar misali ne ga sauran kasashe, a fannin sadaukarwa da juriya, dake kaiwa ga cimma nasarar da ake fata, ta ganin bayan wannan cutar mai hadarin gaske ga rayukan bil Adama.

Saminu Alhassan