logo

HAUSA

Mai Zuma ba ya Talla

2021-01-27 19:48:27 CRI

Mai Zuma ba ya Talla_fororder_微信图片_20210127194806

A yayin da al’ummar duniya suka fara cin gajiyar alluran riga kafin da wasu kamfanonin harhada magunguna ciki har da na kasar Sin suka samar, a hannu guda kuma wasu kasashe na amfani da wannan dama wajen yin takara da kokarin yin fito na fito, maimakon barin kasashe su zabi alluran riga kafin da suka kwanta musu a rai.

Rahotanni daga kasar Indiya na cewa, nan da ’yan makonni masu zuwa ne, ake sa ran kasar ta Indiya za ta samarwa kasashen kudancin Asiya miliyoyin rigakafin na COVID-19, matakin da ake ganin kokari ne na rage tasirin kasar Sin. Ko ma mene ne, ai mai Madi shi ke yin talla ba mai Zuma ba.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, alluran rigakafin cutar ta COVID-19, abu ne mai muhimmanci ga al’ummar duniya. A don haka, tana fata da ma maraba da karin kasashe su gaggauta samar da rigakafi masu tsaro da kuma inganci, su kuma samarwa kasashe masu tasowa, ta yadda karin mutane za su ci gajiyarsu maimakon takara ko ma tilastawa kasashe sayen riga kafin da suka samar.

Yanzu haka, akwai kasashe da dama bisa radin kansu, da suka amince da inganci da tsaron riga kafin kasar Sin, har ma an yiwa shugabannin kasashensu, baya ga ma’aikatansu na lafiya da su ma ake shirin yi musu wannan riga kafi.

Al’ummun kasa da kasa dai na fatan ganin karshen yaduwar wannan annoba. To sai dai kuma duk da riga kafin da aka fara amfani da su a sassan duniya, a hannu guda, ana fuskantar wasu matsaloli game da batun aiwatar da rigakafi. Wannan ne ma ya sa babban daraktan WHO Tedros Ghebreyesus, ya nuna damuwa game da yadda ake rarraba alluran rigakafin, saboda yadda wasu kasashe ke sanya batun siyasa a ciki.

A baya bayan nan, hukumar WHO ta ce tana tantance wasu karin alluran rigakafin COVID-19 iri 13, ciki hadda na kamfanonin Sin 2, kuma 3 na matsayi na 3 na gwaji, wadanda kuma mai yiwuwa a fara amfani da su a lokutan gaggawa.

Don haka, da zarar an kai ga fara amfani da wadannan riga kafi, kamata ya yi a bar kasashe su zabi riga kafi mafi tsaro da inganci da suke bukata bisa radin kansu.

Duk da riga kafin da aka samar da ma wadanda ke hanya, masana a hukumar lafiya ta duniya sun ja hankalin kasashen duniya cewa, kada ma su fara tsammanin ganin bayan annobar ta COVID-19 a cikin wannan shekara ta 2021, domin kawo yanzu a tarihin bil adama cutar kyanda ce kadai aka taba samun nasarar kawar da ita daga doron duniya ta hanyar riga-kafi. Amma kuma duk abin da Daji ya kunsa to da sanin Biri. (Ibrahim Yaya)