logo

HAUSA

Wane irin tsarin cudanyar tattalin arzikin duniya ake bukata?

2021-01-27 20:13:30 CRI

Wane irin tsarin cudanyar tattalin arzikin duniya ake bukata?_fororder_1

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, wasu mutane sun nuna adawa da yunkurin cudanyar tattalin arzikin duniya, ta hanyar fakewa da yaduwar cutar mumfashi ta COVID-19, amma hakika idan ana son ganin bayan annobar, dole ne a kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a cikin jawabinsa a gun taron “Jadawalin Davos” na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya da ake gudanarwa a halin yanzu, kara habaka dunkulewar tattalin arzikin duniya, ita ce za ta kara karfin kawo albarkar zamantakewar al’umma da sakamako na ci gaban kimiyya da fasaha, inda ya ce, dakatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya ta hanyar rufe kofa da raba kai, ta hanyar fakewa da yaduwar annoba, bai dace da moriyar daukacin kasashen duniya ba.

Wane irin tsarin cudanyar tattalin arzikin duniya ake bukata?_fororder_2

An lura cewa, tun bayan barkewar annobar COVID-19, masana kimiyya a fadin duniya suna hada kai domin yin nazari kan allurar rigakafin cutar, kuma akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa yayin da ake jigilar allurar, kana dole ne kasashen duniya su yi kokari tare domin samar da kayayyaki da kuma jigilar kayayyakin, ta yadda za a cimma burin farfafo da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

Jawabin shugaba Xi yayin taron dandalin tattalin arzikin duniya ya gabatar da dabarun kasar Sin kan lamarin.

Abu mai faranta rai shi ne, kasar Sin tana kokari matuka domin cimma yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Kawo yanzu kasar Sin ta samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga kasashe sama da 150 da kungiyoyin kasa da kasa 13, kuma ta aika tawagogin likitoci ga kasashen da suke da bukata har sau 36.

Ban da haka, a kokarin da ake na magance rashin daidaito wajen ci gaban kasa da kasa, a ko da yaushe kasar Sin tana aiwatar da manufar bude kofa ga ketare, domin tabbatar da zaman karko a bangaren samar da kayayyaki a fadin duniya, kana ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya domin ingiza ci gaban kasashen duniya baki daya.

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana kokarin daga matsayinta na bude kofa ga ketare, domin samar da karin damammakin hadin gwiwa ga kasashen duniya, tare kuma da kara kuzari kan farfadowa da karuwar tattalin arzikin duniya.(Jamila)