MDD: ’Yan Sudan ta kudu miliyan 8.3 ne ke bukatar tallafin jin kai
2021-01-27 10:06:58 CRI
Ofishin tsare-tsare na ayyukan jin kai na MDD ko OCHA, ya ce daga bara zuwa yanzu, adadin ’yan Sudan ta kudu dake cikin yanayi na bukatar agajin jin kai, ya karu daga mutum miliyan 7.5 zuwa miliyan 8.3. Ofishin OCHA ya ce adadin na karuwa, duk da cewa adadin daukacin ’yan kasar bai wuce kusan mutum miliyan 11 ba.
Wata sanarwar da OCHA ta fitar, ta dora alhakin aukuwar hakan kan shekaru da dama da kasar ta shafe tana fama da tashe-tashen hankula, da sauyin yanayi, kafin kuma ta tsunduma cikin annobar COVID-19. Ofishin ya ce cikin wadanda ke neman agajin na gaggawa, har da mutane 310,000 dake gudun hijira da masu neman mafaka.
Sanarwar ta ce yunwa na karuwa a kasar, inda ake hasashen sama da ’yan Sudan ta kudun miliyan 7.2 na cikin barazanar fuskantar karancin abinci mai tsanani a wannan shekara ta 2021.
Sudan ta kudu, daya daga kasashe mafiya kankantar shekaru a duniya, ta samu ’yancin kai ne a shekarar 2011. Kuma duk da kasancewar kasar mai arzikin mai, a hannu guda, tana cikin kasashe mafiya talauci a duniya, inda take matsayi na 157 cikin kasashe ko yankuna 194 mafiya fatara, wadanda asusun IMF ya lasafta a bara, cikin rahotonsa na hasashe da ya saba fitarwa. (Saminu Hassan)