logo

HAUSA

Xi Jinping ya samar da shirin kasar Sin kan yadda za a kara yin yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban

2021-01-27 09:31:10 CRI

A ranar Litinin 25 ga wata ne, aka bude taron dandalin tattalin arziki na duniya (WEF) a birnin Davos, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi Jinping ya samar da shirin kasar Sin kan yadda za a kara yin yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban_fororder_20210127世界21004-hoto2

A jawabin da ya gabatar, Xi ya bayyana cewa, babu tantama daukacin bil-Adama za su samu nasara kan kwayar cutar COVID-19, har ma su farfado yadda ya kamata daga wannan annoba. Ya ce “Har yanzu ba mu kai ga ganin wannan annoba ba. Yadda ake kara samun masu kamuwa a baya-bayan, ya kara tunanar da mu cewa, wajibi ne mu ci gaba da yaki da ita”

Xi ya ce, kowa ce kasa ta sha bamban kan yanayin tarihinta, al’adu da tsarinta na zamantakewa, kuma babu wanda ya fi wani. Ya kuma yi gargadi kan duk wani kokari na tilasta matsayi kan wayewar kai ko tilsatawa wani tarihi, ko al’ada ko tsarin zamantakewarsa kan wasu. “Kasashe na da ’yancin zabin kasancewa tare ta hanyar mutunta juna da neman matsaya yayin warware bambance-bambance, da yayata musaya da koyi da juna. Wannan ita ce hanyar kara samun ci gaban da aka samu a wayewar kan bil-Adama.”

Xi Jinping ya samar da shirin kasar Sin kan yadda za a kara yin yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban_fororder_20210127世界21004-hoto3

Ya ce, ya kamata kasashen duniya, su kara mayar da hankali, su girmama kudirinsu, su kuma baiwa kasashe masu tasowa goyon bayan da ya kamata, da kare zabinsu na samun ci gaba. Shugaba Xi ya ce, ya kamata a karfafa batun samar da ‘yanci da damammaki da dokoki daidai wa daidai, ta yadda dukkan kasashe za su amfana daga damammaki da sakamakon ci gaba da aka samu.

Xi ya jaddada cewa, babu wata kasa ita kadai da za ta iya magance matsalar da duniya ke fuskanta, wajibi ne kasashen duniya su hada kai, su dauki mataki tare da yin hadin gwiwa.

Idan har aka fara gina kananan kawance ko fara wani salo na yakin cakar baka, hakan zai raba kan duniya har ma ya haifar da yin fito na fito. A don haka, ya yi gargadi kan yin watsi, ko barazana ko tursasawa wasu, tilasta kwaikwayon wani abu, da katse hanyoyin samar da kayayyyaki ko sanya takunkumi da zama saniyar ware ko katse hulda. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)