logo

HAUSA

Wane Irin Tsarin Hadin Gwiwa Ake Bukata Tsakanin Sassa Daban Daban? Sin Tana Da Amsa

2021-01-26 16:15:46 CRI

Wane Irin Tsarin Hadin Gwiwa Ake Bukata Tsakanin Sassa Daban Daban? Sin Tana Da Amsa_fororder_210126-sharhi-maryam-hoto

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi ta kafar bidiyo cikin taron ajandar Davos, inda ya bayyana ra’ayinsa kan irin tsarin hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban na duniya da ake bukata, inda kuma ya fidda dabaru kan yadda za a yi yaki cutar COVID-19 cikin hadin gwiwar kasa da kasa, da farfado da tattalin arzikin duniya, da kuma yadda za a gudanar da harkokin kasa da kasa bayan annobar.

Xi Jinping ya ce, bai kamata a fake da wannan ra’ayi, don daukar matakai na kashin kai ba, kuma, ya kamata a fidda sabbin hanyoyi cikin adalci domin neman makoma mai kyau. Jawabin da ya bayar, ya fidda dabaru ta fuskar aiwatar da tsarin hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban, da nuna muhimmin ma’anar raya wannan tsari.

Bugu da kari, kasar Sin tana aiwatar da tsarin hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban yadda ya kamata, bisa ga yadda take neman karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da COVID-19, da aiwatar da tsarin bude kofa ga waje domin cimma moriyar juna, da kuma inganta ayyukan neman dauwamammen ci gaba da dai sauransu. Kana, gamayyar kasa da kasa sun ji aniyar kasar Sin ta tsayawa tsayin daka kan tsarin hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban bisa jerin matakan da shugaba Xi ya gabatar cikin jawabinsa.

Shi ya sa, shugabar kwalejin nazarin tattalin arziki da kasuwanci ta jami’ar Witwatersrand ta kasar Afirka ta Kudu, Jannie Rossouw ta bayyana cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannin karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, kuma tana da imanin cewa, a nan gaba, tabbas, Sin za ta ba da karin gudummawa a wannan fanni. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)