logo

HAUSA

Kwararru: Jawabin shugaba Xi Jinping yana da ma’ana matuka

2021-01-26 13:50:38 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron dandalin tattalin arziki na duniya (WEF) ta kafar bidiyo a jiya Litinin, inda ya yi wani jawabi mai taken “Yin amfani da ra’ayi na kasancewar bangarori masu fada a ji daban daban a duniya, wajen taimakawa dan Adam samun ci gaba”.

A ganin wasu kwararru masu nazarin al’amuran duniya, jawabin shugaba Xi yana da ma’ana matuka.

Madam Su Xiaohui, mataimakiyar darektar sashen nazarin kasar Amurka ce, a karkashin cibiyar nazarin al’amuran kasa da kasa ta kasar Sin. A cewarta, shugaba Xi ya yi bayani kan wasu matsalolin dake addabar kasashe daban daban a wannan zamanin da muke ciki. Ta ce,

“Shugaba Xi ya ce, wata babbar matsalar da mutanen duniya suke fuskantar ita ce sabanin ra’ayi a fannin tsare-tsaren siyasa. A cewarsa, wannan batu ya haddasa matsalar tsaro, da raunana huldar dake tsakanin kasashe daban daban, da haifar da kalubale ga yunkurin al’ummun kasashe daban daban na yin hadin gwiwa a tsakaninsu, da kafa wata al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Kana wata matsala ta daban ita ce, gibin da ake samu tsakanin kasashe daban daban ta fuskar samun ci gaba. Annobar COVID-19, da matakan kashin kai, da kariyar ciniki da wasu kasashe suka dauka, sun tsawaita gibin da ake samu tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa, lamarin da ka iya zama shinge ga tattalin arzikin duniya dake kokarin neman farfadowa.”

A nashi bangare, mataimakin shugaban kwalejin nazarin ilimin diplomasiyya, Gao Fei, ya ce, shugaba Xi Jinping ya ambaci manyan matsalolin da duniya ke fuskanta a cikin jawabinsa, musamman ma matsalar da ta shafi batun ci gaban al’umma. Ya ce,

“Sakamakon annobar COVID-19, duniyarmu na fuskantar tarin matsaloli, musamman ma a fannin samun ci gaban al’umma. Yanzu gibin da ake samu tsakanin tattalin arzikin kasashe masu tasowa da na kasashe masu sukuni, maimakon ya ragu, ya sake karuwa sosai. Kuma muddin akwai wannan gibi, to, duniyarmu za ta ci gaba da fuskantar manyan matsaloli daban daban da suka ki ci suka ki cinyewa.”

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya nanata cewa, ko da yake matsalolin da ke addabar al’ummun duniya suna da sarkakiya, amma akwai mafita, wadda ita ce karewa, tare da aiwatar da ra’ayi na kasancewar bangarori masu fada a ji daban daban a duniya, da kokarin kafa wata al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Madam Su ta yi tsokaci kan maganar shugaba Xi dangane da ra’ayin kasancewar bangarori daban daban. Ta ce,

“An bayyana ra’ayi na kasar Sin sarai, wato karewa, tare da aiwatar da ra’ayi na kasancewar bangarori masu fada a ji daban daban a duniya. Kana shugaba Xi ya bayyana yadda ake kallon wannan ra’ayi a kasar Sin. Ya ce bai kamata ba a fake da wannan ra’ayi, don daukar matakai na kashin kai. Hakika ana bukatar tsayawa kan ra’ayin nan na kasancewar bangarori masu fada a ji da yawa a duniya, idan har ana son samun ci gaban al’ummun duniya a nan gaba.”

Lokacin da ya ambaci matakan da kasar Sin za ta dauka, shugaba Xi Jinping na kasar ya ce, kasarsa za ta ci gaba da kokarin hadin gwiwa tare da sauran kasashe, don dakile cutar COVID-19, da aiwatar da manufar bude kofar gida ga kasashen ketare don tabbatar da moriyar kowa, da kara kokarin neman samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa, da kirkiro karin sabbin fasahohi, da taka rawa a fannin kulla sabon nau’in huldar kasa da kasa. A cewar mista Gao Fei, kasar Sin za ta cika alkawarin da ta dauka,

“Idan mun waiwayi jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi a taron dandalin DAVOS na shekarar 2017, za mu ga yadda ya yi hasashen yanayin da muke ciki a yanzu. Cikin wadannan shekaru 4 da suka wuce, al’ummun duniya sun tinkari wasu manyan kalubaloli. Sai dai ta la’akari da wannan yanayin da muke ciki, shin wadanne matakai ne za mu iya dauka a nan gaba? Hakika muna iya ganin dorewar manufar kasar Sin a nan: Ta yi alkawari, daga baya ta cika shi, sa’an nan za ta ci gaba da tsayawa kan manufarta a nan gaba.” (Bello Wang)

Bello