logo

HAUSA

Ko akwai yiyuwar kyautata hulda tsakanin Amurka da Turai bayan sabon shugaban kasar ya fara rike mulki?

2021-01-25 19:01:57 CRI

Wasu kafofin watsa labarai na kasashen Turai sun taba yin sharhi kan huldar dake tsakanin kasar Amurka da kasashen Turai kamar haka: suna gudanar da dangantakarsu ce ta hanyar yin amfani da na’urorin taimakawa yin numfashi, tsokacin da ya nuna cewa, suna bata rai matuka kan huldar, yanzu an kammala mika mulki a Amurka, ko akwai yiyuwar kyautata huldar dake tsakanin sassan biyu bayan sabon shugaban kasar ta Amurka ya fara aiki?

Ko akwai yiyuwar kyautata hulda tsakanin Amurka da Turai bayan sabon shugaban kasar ya fara rike mulki?_fororder_1

Duk da cewa, shugaban Amurka Joe Biden ya taba bayyana cewa, zai yi kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasarsa da kasashen Turai, amma sabon sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya yi tsokacin cewa, gwamnatin Amurka za ta dakatar da kammala aikin gina bututun iskar gas na Nord Stream-2, lamarin da ya sa kasashen Turai ba za su ji dadi ba, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ita ma ta mayar da martani cewa, “zai yi wahala a kyautata huldar dake tsakanin Amurka da Turai.”, kana ta taba bayyana cewa, ba za ta cimma matsaya guda tsakaninta da Biden kan daukacin al’amura ba, ita ma ba za ta bar aikin Nord Stream-2.

Ko akwai yiyuwar kyautata hulda tsakanin Amurka da Turai bayan sabon shugaban kasar ya fara rike mulki?_fororder_2

Aikin Nord Stream-2 da kasashen Turai da kasar Rasha suke gudanarwa cikin hadin gwiwa yana shafar tsaron makamashi na kasashen Turai, amma Amurka tana son dakatar da aikin domin sayar da iskar din ta gas a kasashen Turai, a don haka shugabannin kasashen Turai sun nuna rashin jin dadinsu.

A bayyane take cewa, zai yi wahala a kyautata huldar dake tsakanin Amurka da kasashen Turai, duk da cewa, sabon shugaban Amurka ya fara aiki a kasar.

Dalilin da ya sa haka shi ne, ba abu ne mai sauki ba sassan biyu su daidaita tsoffin matsalolin da suke fuskanta, kuma a halin yanzu Amurka ta fi mai da hankali kan yankin tekun Indiya da na Pasifik, a maimakon nahiyar Turai, shi ya sa ba zai yiyu ba Amurka ta kara zuba jari ga kasashen Turai ko a bangaren tattalin arziki, ko a bangaren aikin soja.

Ana iya cewa, babban sabanin dake tsakanin sassan biyu, zai haifar da babbar matsala yayin da suke gudanar da huldar dake tsakaninsu.(Jamila)