logo

HAUSA

Sin ta zama babbar kasa ta farko da ta jawo jarin waje a duniya a bara

2021-01-25 12:19:33 CRI

Sin ta zama babbar kasa ta farko da ta jawo jarin waje a duniya a bara_fororder_A

Jiya Lahadi, hukumar raya kasuwanci da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya ko kuma UNCTAD a takaice, ta bullo da sabon rahoto game da sa ido kan harkokin zuba jari na duk duniya, rahoton ya nuna cewa, a bara, yawan jarin wajen da aka zuba kai-tsaye a duk duniyar ya ragu da kaso 42 bisa dari, inda har ma aka yi kiyasin cewa, a bana, adadin zai dada raguwa. Amma a bangaren Sin, karo na farko ta zarce kasar Amurka, inda har ta zama ta farko wajen jawo jarin waje a duniya.

Sashin kula da zuba jari da kamfanoni na hukumar UNCTAD Mista Zhan Xiaoning, ya zanta da wakiliyar babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, inda ya ce, yawan jarin wajen da aka zuba kai-tsaye a duniya bai wuce dala biliyan 859 kacal ba a bara, adadin da ya ragu da kaso 42 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekara ta 2019, wanda ya kai dala triliyan 1.5. Mista Zhan ya bayyana cewa:

“Raguwar ta fi damun kasashe masu hannu da shuni, inda yawan jarin wajen da aka zuba kai-tsaye a kasashen ya ragu da kaso 69%, wanda bai wuce dala biliyan 229 kacal ba, adadin da ya zama mafi muni a shekaru 25 da suka gabata. Sa’an nan yawan jarin wajen da aka zuba kai-tsaye a kasashe masu tasowa ya ragu da kaso 12%, wanda ya kai dala kimanin biliyan 616, adadin da ya dauki kaso 72% na yawan jarin wajen da aka zuba kai-tsaye a duk duniya, wanda ya kai matsayin koli a tarihi. Game da wasu manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, ciki har da Birtaniya, da Italiya, da Rasha, da Jamus, da Brazil da kuma Amurka, yawan jarin wajen da aka zuba musu ya ragu ainun, yayin da aka samu karuwa a kasashen Sin da Indiya.”

Game da su kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai wato EU, Mista Zhan ya yi karin haske cewa:

“Yawan jarin wajen da aka zuba kai-tsaye a kasar Amurka ya ragu da kaso 49% a bara, wanda ya kai dala kimanin dala biliyan 130. Haka kuma yawan jarin da kamfanonin waje suka zuba don fara kasuwanci gami da sana’ar sayen kamfanoni duk sun ragu a Amurka, musamman kamfanonin kasashen Birtaniya da Jamus da Japan, wato yawan jarin da suka zuba a Amurka ya ragu kwarai da gaske. A bangaren Birtaniya ma, yawan jarin wajen da aka zuba kai-tsaye a kasar bai karu ko kadan ba, sakamakon yaduwar annobar COVID-19 a duniya, gami da ficewar ta daga tarayyar Turai wato EU.”

Mista Zhan ya ci gaba da cewa, a bara, kasar Sin ta yi nasarar shawo kan munanan illolin da annobar COVID-19 ta haifar, har ma yawan jarin da ta jawo kai-tsaye daga kasashen waje ya samu karuwa sosai. Zhan ya ce:

“Bisa hasashen da hukumar UNCTAD ta yi, a shekarar da ta gabata, yawan jarin wajen da kasar Sin ta yi amfani da shi ya karu da kimanin kaso 4%, wanda ya kai dala biliyan 163, ciki har da jarin da aka zuba a bangaren hada-hadar kudi. Kana, yawan jarin wajen da ta janyo shi ma ya kai matsayin koli a tarihi, wato ta zarce Amurka, har ta zama ta farko a duk fadin duniya baki daya. Ni kuma na yi nazarin cewa, adadin jarin wajen da kasar Sin ta janyo ya kai kaso 19 a duk fadin duniya. Tattalin arzikin kasar ma ya samu farfadowa da karuwa, al’amarin da ya jawo hankalin kasa da kasa. A yayin da ake fama da cutar COVID-19, kamfanonin kasa da kasa sun dogara sosai kan sana’o’in masana’antunsu a kasar Sin, abun da ya taimaka ga bunkasar jarin waje a kasar. A bangaren gwamnati ma, tana daukar wasu matakai da dama wajen saukaka matakan zuba jari da kasuwanci, don taimakawa bunkasar jarin waje.”

Mista Zhan Xiaoning ya yi taka-tsantsan game da makomar zuba jari a duniya, inda a cewarsa, a shekarar da muke ciki, harkokin zuba jari na kai-tsaye a duniya za su ci gaba da fuskantar koma-baya. Zhan ya ce:

“Ga alama dai, za’a kawo karshen raguwar jarin da ake zubawa kai-tsaye a duniya a karshen rabin shekarar da muke ciki, watakila kuma za a samu murmurewa a shekara ta 2022. Akwai kalubaloli da dama wadanda za su kawo cikas ga farfadowar harkokin zuba jari a duniya, ciki har da hadarin dake tattare da sabuwar barkewar annobar COVID-19, da tafiyar-hawainiya game da gudanar shirin yin allurar riga-kafin cutar, da shirin goyon-bayan tattalin arziki, da kuma rashin sanin tabbas game da manufofin zuba jari a duniya.” (Murtala Zhang)