logo

HAUSA

Murtala Sabo Sagagi: Sin abar koyi ce a fannin kawar da talauci da yaki da COVID-19

2021-01-25 14:15:38 CRI

Murtala Sabo Sagagi: Sin abar koyi ce a fannin kawar da talauci da yaki da COVID-19_fororder_微信图片_20210125132532

Prof. Murtala Sabo Sagagi, malami ne dake koyarwa a makarantar koyon kasuwanci da sana’o’i wato Dangote Business School dake jami’ar Bayero a jihar Kano, kana masanin tattalin arziki a tarayyar Najeriya.

A hirarsa da Murtala Zhang, ya bayyana ra’ayinsa kan sirrin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, duk da cewa duniya na fuskantar barazanar yaduwar annobar COVID-19. Ya kuma ce kasar Sin ta samu manyan nasarori a fannonin kawar da fatara da yaki da cutar. Don haka, ta cancanci a yi koyi da ita.

Prof. Murtala Sagagi ya yi tsokaci kan yarjejeniyar gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci ta nahiyar Afirka, wadda ta fara aiki a farkon watan Janairun bana. Ya kuma taya kasashen Sin da Najeriya murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu. (Murtala Zhang)