logo

HAUSA

Sin Tana Kokarin Cimma Burin Raya Wasannin Kankara A Kasar

2021-01-24 21:39:45 CRI

Sin Tana Kokarin Cimma Burin Raya Wasannin Kankara A Kasar_fororder_0124-2

Tabbatar da mutane miliyan 300 sun yi wasan kankara shi ne alkawarin da Sin ta yiwa kasa da kasa yayin da birnin Beijing da Zhangjiakou suke kokarin share fagen bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022. A halin yanzu, ana kusa da gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, jama’ar kasar Sin suna kara son wasannin kankara.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar farko a cikin kasar a shekarar 2021 a yankunan shirye-shiryen gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu a birnin Beijing da lardin Hebei, inda kuma ya gaisa da ‘yan wasa, da masu bayar da horo, gami da ma’aikatan dake tabbatar da nasarar ayyukan wurin wasanni na Zhangjiakou, da kuma wakilan ma’aikatan gine-gine.

A sakamakon samun iznin daukar bakuncin gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, Sin ta samu babbar damar raya wasannin kankara, kana ta yi kokarin shigar da aikin raya wasannin kankara zuwa aikin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. Fatan shugaban kasar Sin Xi Jinping a wannan fanni ya zarce burin bunkasa wasan kankara kawai.

Bisa kididdigar da aka yi, ya zuwa watan Oktoba na shekarar 2018, mutane fiye da miliyan 50 na kasar Sin sun shiga wasan kankara kai tsaye. Kana a shekarar 2019 zuwa 2020, mutane kimanin miliyan 150 na kasar Sin sun halarci wasan kankara. A halin yanzu, wasan kankara ya riga ya zama daya daga cikin wasannin motsa jiki ko hanyoyin rayuwa na Sinawa.

Ban da wannan kuma, raya sha’anin wasan kankara zai zama sabon karfi na bunkasa tattalin arzikin kasar Sin. Bisa rahoton raya yawon shakatawa dake da nasaba da wasan kankara na kasar Sin na shekara 2020, an ce, yawan mutanen Sin dake yawon shakatawa dake da nasaba da wasan kankara a kowace shekara yana ci gaba da karuwa, kashi 61.5 cikin 100 na Sinawa sun taba yin wasan kankara. Yawan kudin da kowane mutum ya kashe a wannan fanni tun daga shekarar 2018 zuwa 2019 ya kai 1734. Yawon shakatawa dake da nasaba da wasan kankara ya riga ya zama wata hanyar yin rayuwa ta jama’ar kasar Sin, kuma Wannan fanni ya zama daya daga cikin muhimman fannoni da mutane ke kashe kudi a yau da kullum.

A matsayin sabuwar kasar dake kokarin raya wasan kankara, yawan mutanen Sin da ke yawon shakatawa dake da nasaba da wasan kankara ya zarce miliyan 200. Sin tana kokarin cimma alkawarinta da aka yi yayin da take neman iznin samun damar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, kuma yanzu Sin tana kusa da cimma wannan buri. (Zainab)