logo

HAUSA

Alluran Rigakafin Kasar Sin Sun Sanya Kwarin Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 A Kasashe Da Yankuna Masu Yawa

2021-01-23 18:36:05 CRI

Alluran Rigakafin Kasar Sin Sun Sanya Kwarin Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 A Kasashe Da Yankuna Masu Yawa_fororder_320

Annobar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, bisa wannan yanayin da ake ciki, ana daukar alluran rigakafi a matsayin makami mai karfi na yaki da annobar. A halin yanzu, ingancin alluran rigakafin kirar kasar Sin da amfaninsu,sun samu amincewa sosai, har ma kasashe da yankuna da dama sun amince da rajistar alluran rigakafin na kasar Sin don tallatawa ko amfani da su cikin gaggawa. Kasashe da yankuna da yawa a duniya, sun cimma yarjejeniyar sayen alluran rigakafi na kasar Sin. Ana iya gano cewa, allurar rigakafin ta kasar Sin ta bada kwarin gwiwa ga kasashe da yankuna da dama game da yaki da annobar COVID-19.

Ko allurar rigakafin na da inganci ko a’a? Kuma amfanin alluarar na kwana nawa ne? Shin ana iya jigilar allurar cikin sauki? Wadannan su ne muhimman ma’aunin tantance ingancin allurar rigakafi. Ma’aunin alluran rigakafin kirar kasar Sin ko a fannin inganci ko kuma a fannin amfani, dukkansu sun zarce matsayin da hukumar WHO ta tsara. Bugu da kari, adana alluran rigakafin kasar Sin da jigilar su, sun dace da yanayin yawancin kasashe. Bayanai sun tabbatar da ingancin alluran rigakafin kasar Sin.

Alluran Rigakafin Kasar Sin Sun Sanya Kwarin Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 A Kasashe Da Yankuna Masu Yawa_fororder_src=http___z1.dfcfw.com_2020_5_30_20200530122501403992510_o&refer=http___z1.dfcfw

A yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 20 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta yi tsokaci kan shirin COVAX, inda ta ce, gwamnatin kasar na sa himma da gwazo wajen goyon bayan kamfanonin samar da alluran rigakafi na kasar su shiga shirin nan, tare da taimaka musu a fannin. Ya zuwa yanzu, kamfanonin da suka hada da Sinopharm, Sinovac da CanSinoBIO da dai sauransu, sun riga sun gabatar da bukatarsu ga masu kaddamar da shirin a hukumance.

Ta hanyar aiwatar da hakikanan ayyuka, kasar Sin tana cika alkawarinta na sanya alluran rigakafin zama kayan amfanawa jama'ar duniya. Tana kuma more nasarorin da ta cimma kan nazarin alluran rigakafin tare da kasashe daban daban, hakan ya kuma kara kwarin gwiwa ga wasu kasashe da dama wajen shawo kan annobar ta COVID-19, da kuma kawo fatan samun makoma mai kyau na farfado da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma. (Bilkisu Xin)