logo

HAUSA

Ya kamata a yi kokari tare don dawo da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka

2021-01-22 13:40:05 CRI

A ranar 20 ga wata, sabon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi rantsuwar kama aiki. Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, zai gyara wasu manufofin cikin gida da wajen kasar. Shin ko sabbin manufofin da zai gabatar game da kasar Sin zai janyo hankalin kasa da kasa sosai.

A cikin shekaru 4 da suka gabata, Sin da Amurka sun fuskanci mawuyacin hali. Saboda ra’ayin wasu ‘yan siyasar Amurka dake Washington na yakin cacar baki da bambancin ra’ayi kan kasar Sin, inda suka maida kasar Sin a matsayin babbar barazana, da zargin tsarin siyasa na kasar Sin, da hana ci gaban kamfanonin kasar Sin, da gudanar da ayyuka sau da dama don kawo illa ga moriyar kasar Sin da batutuwan da suka shafi Sin, hakan ya bata imanin dake tsakanin Sin da Amurka, da kuma kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na duniya.

Game da kyautata yanayin dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, a karshen watan Nuwanba na shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bugawa Joe Biden waya, don taya masa murnar zama sabon shugaban kasar Amurka, inda ya bayyana fatan kasashen biyu, za su daina nuna kiyayya da juna, da girmama juna, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, da maida hankali ga hadin gwiwarsu da daidaita matsalolin dake tsakaninsu don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata. Wannan ya shaida cewa, maganar da shugaba Xi Jinping ya yi ta bayyana matsalolin dake kawo cikas ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kana ya bayyana hanyar kyautata dangantakarsu da daina wannan hali.

Yayin da manyan kasashen suke yin mu’amala, ya kamata a girmama juna. A sakamakon ayyukan da wasu ‘yan siyasa na kasar Amurka suka yi a shekaru 4 da suka gabata, sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta nuna cewa, dakatar da yin ayyukan dake kawo illa ga dangantakar dake tsakaninta da Sin, shi ne sharadin sa kaimi ga mayar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Bisa yanayin da ake ciki, ya kamata bangarorin biyu su bullo da hanyoyi da tsarin yin mu’amala mai dacewa, da gabatar da ra’ayin kyautata dangantakar dake tsakaninsu, hakan zai taimaka ga raya dangantakarsu.

A hakika, tarihi ya nuna cewa, koda yake Sin da Amurka suna da bambanci a fannonin tsarin zamantakewar al’umma, da matakin bunkasuwa, da al’adu da sauransu, amma moriya iri daya da suke da ita, ta fi bambancin dake tsakaninsu, don haka hadin gwiwa ita ce hanya daya tilo ta daidaita matsalolinsu. Sin da Amurka suna da babbar damar hadin gwiwa a fannonin magance yaduwar cutar COVID-19, da farfado da tattalin arziki, da tinkarar sauyin yanayi da sauransu, hakan zai zama hanya mafi dacewa wajen sake nuna imani da juna.

Bayan da Biden yayi rantsuwar kama aiki, ya sanar da matakai da dama na yaki da cutar COVID-19, ciki har da dakatar da janyewar kasar daga hukumar WHO. Kana ya sa hannu kan umurnin dawo da kasar cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris.

Wannan ya shaida cewa, yayin da Sin da Amurka suke yin kokari tare, za a gudanar da ayyukan dake kawo moriya ga dukkan duniya. Idan kasashen biyu suka nuna kiyayya da juna, hakan zai iya kawo illa ga al’ummar duniya baki daya. Idan ana son mayar da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, ya kamata kasashen biyu su yi kokari tare.

A halin yanzu, Sin da Amurka suna tsaye a sabon wurin inda hanyoyi suka gitta juna. Koda yake akwai bambanci a tsakaninsu, amma bai kamata su nuna kiyayya ga juna ba, ya kamata su yi hadin gwiwa don warware matsalolinsu. Sin ta riga ta gabatar da shawarwarin bude dukkan hanyoyin yin mu’amala, da tattauna jerin ayyukan yin mu’amala, da maida hankali ga yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar COVID-19. Sin na fatan sabuwar gwamnatin kasar Amurka, za ta hada kai da ita, don rubuta wani sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, wanda zai dace da moriyar jama’ar kasashen biyu, da kuma ba da gudummawa ga dukkan duniya baki daya. (Zainab)