logo

HAUSA

Sanya takunkumi kan Pompeo da sauran wasu Amurkawa 27 abu ne da ya dace

2021-01-22 18:54:30 CRI

Sanya takunkumi kan Pompeo da sauran wasu Amurkawa 27 abu ne da ya dace_fororder_A

Kwanan nan, gwamnatin kasar Sin ta sanar da sanya takunkumi kan wasu Amurkawa guda 28, wadanda take tuhumarsu da aikata laifin karya dokokin ikon kasar, kuma su ne ke da alhakin laifuffuka da dama da Amurka ta aikata ga kasar Sin. Mutanen sun hada da wasu masu karfin fada-a-ji a gwamnatin Donald Trump, ciki har da Mike Pompeo.

Kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce, a ’yan shekarun da suka gabata, wasu masu adawa da manufofin siyasar kasar Sin dake Amurka, sun kulla makirci da kaddamar da munanan kudurori, gami da yin shisshigi a cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, a wani kokari na biyan bukatun siyasa na kashin kansu gami da nuna kiyayya ga kasar Sin. Aika-aikar da suka yi ta lahanta moriyar kasar Sin, da bakanta ran al’ummar kasar, tare kuma da haifar da mummunar illa da koma-baya ga huldar dake kasancewa tsakanin Sin da Amurka.

Muna iya gano cewa, Amurkawan da kasar Sin ta sanyawa takunkumi a wannan karo, kusan dukkansu manyan jiga-jigai ne a cikin gwamnatin Trump. Irin wannan abun da kasar Sin ta yi, ya shaidawa mutanen kasashen waje dake kyamar kasar Sin babbar niyyar gwamnatin kasar, wato kare ikon mulkin kai da moriyar ci gaba.

Sanya takunkumi kan Pompeo da sauran wasu Amurkawa 27 abu ne da ya dace_fororder_B

Wani abun lura na daban shi ne, takunkumin da aka sanyawa Amurkawan 28, ba takunkumi ne da ya shafi kansu kawai ba, har ma da ’yan uwansu, gami da kamfanonin dake da alaka da su, wato an hana su yin mu’amalar ciniki da kasar Sin. Bisa al’ada, bayan da jami’an gwamnati ko kuma sanatoci suka yi ritaya a Amurka, su kan shiga wasu kamfanoni, ko kuma cibiyoyin dake da alaka da su don samun aikin yi ko kudi. Takunkumin da kasar Sin ta sanya musu a wannan karo, ya tabbatar da cewa, duk wani kamfani ko kuma cibiya, idan suka dauki hayar wadannan ’yan siyasa, ba za su iya samun damar yin kasuwanci da bangaren kasar Sin ba. Tamkar abun da malam Bahaushe kan ce, kowa ya shuka zamba, shi zai girba.

Yanzu haka sabuwar gwamnatin Joe Biden ta kama aiki a Amurka. Duk da cewa ba za ta yi fatali da manufarta ta hana ci gaban kasar Sin ba, amma irin takunkumin da kasar Sin ta sanyawa Mike Pompeo, da sauran wasu Amurkawa 27, tamkar alamar gargadi ce ga gwamnatin Biden. Wato kamata ya yi Amurka ta fahimci cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta da rauni, kuma duk wata kasa da ta lahanta babbar moriyarta, za ta dandana kudarsa ba kadan ba.

Kwararru da masana na kasa da kasa sun sha bayyana cewa, Sin da Amurka, manyan kasashe biyu ne mafi karfin tattalin arziki a duk fadin duniya. Idan sun hada kawunansu yadda ya kamata, za’a haifar da abubuwan kirki da yawa ga duniya. Amma idan sun rika yiwa juna kiyayya da ja-in-ja tsakaninsu, za’a yi babbar illa ga kasa da kasa. Don haka muna fatan sabuwar gwamnatin Biden za ta gyara kura-kuran da tsohuwar gwamnati ta Trump ta aikata ba tare da bata lokaci ba, da bada hadin-kai ga kasar Sin, domin kawo alfanu ga duk duniya baki daya.  (Murtala Zhang)