logo

HAUSA

Yaya Za A Kawar Da Damuwar Tedros Adhanom Ghebreyesus? Kasar Sin Ta Bada Amsa

2021-01-22 22:25:21 CRI

Yaya Za A Kawar Da Damuwar Tedros Adhanom Ghebreyesus? Kasar Sin Ta Bada Amsa_fororder_微信图片_20210122221751

Bayyanar alluran riga kafin annobar COVID-19 ba shakka labari ne mai kayatarwa, amma akwai tazara tsakanin mawadata da matalauta wajen karbar wannan "maganin cuta".

Yaya hali mai tsananin yake na rarraba allurar rigakafi a duk duniya? Kuma alluran rigakafi nawa wata kasa mai karancin kudi za ta iya samu? Babban daraktan kungiyar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, a kwanan nan ya bayyana cewa, kasashe masu arziki 49 sun karbi alluran rigakafi sama da miliyan 39, amma wasu kasashen da ba su ci gaba ba, suna da allura 25 kacal. Kafafen yada labarai da dama sun ruwaito cewa, mutane 25 ne kacal a kasar Guinea, ciki har da shugaban kasar, aka yiwa rigakafin.

"Ba miliyan 25 ba, ba 25,000 ba, 25 kacal! Ina so in fada a bayyane cewa, duniyar da muke ciki tana gab da fadawa cikin mummunan halin dabi'a." Tedros ya nuna damuwa sosai a kan hakan.

Yaya Za A Kawar Da Damuwar Tedros Adhanom Ghebreyesus? Kasar Sin Ta Bada Amsa_fororder_微信图片_20210122221759

Rarraba allurar rigakafi, ya zama aiki na adalci, da ba da fifiko ga mutanen da suka fi bukata a kasashe daban daban, da kuma baiwa mutanen dake a kasashe masu karamin karfi damar samun rigakafi da wuri-wuri. Wannan shi ne ainihin aniyar WHO, don hakan ne kuma sauran hukumomi suka bullo da shirin COVAX.

Amma gaskiyar ita ce: daga samarwa zuwa saye, masu son alluran rigakafi suna karfafa rashin daidaito tsakanin kasashe masu arziki da matalauta.

Ganin yadda annobar ke addabar duniya, bil Adama na bukatar hadin kai ba tare da la’akari da iyakokin kasa ba, don tinkarar yaduwarta. Game da wannan, kasar Sin tana aiki yadda ya kamata.

Yaya Za A Kawar Da Damuwar Tedros Adhanom Ghebreyesus? Kasar Sin Ta Bada Amsa_fororder_微信图片_20210122221803

A yanzu haka, kasashen Chile, UAE, Bahrain, Masar, Jordan, Turkey, Indonesia, Brazil da sauran kasashe sun amince da amfani da alluran rigakafin kasar Sin. Bisa kididdigar da ba a kammala ba, kasashe sama da 40 sun nemi shigar da alluran rigakafi kirar kasar Sin cikin kasashen su. Shugabannin kasashe da dama da suka hada da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, da shugaban Seychelles Wavel Ramkalawan, da firaministan kasar Jordan Bisher Al Khasawneh, da shugaban Indonesiya Joko Widodo, an yi musu alluran rigakafin kasar Sin a bayyane.

Annobar na yaduwa a duniya, kuma babu wata kasa da za ta iya rayuwa ita kadai. "Ra’ayin son kai kan alluran rigakafi" ba zai iya magance cutar ba, lokaci ya yi da za a hada kai. Wannan magani ne mai amfani don saukaka damuwar Tedros. Kawai bukatar kasashe mafi yawa su gudanar da irin "ayyukan kasar Sin" don yaki da annobar tare. (Mai fassara: Bilkisu)