logo

HAUSA

Jarin waje da aka zuba a Sin ya kafa wani sabon matsayi

2021-01-21 14:00:48 CRI

Jarin waje da aka zuba a Sin ya kafa wani sabon matsayi_fororder_微信图片_20210121140024

Jiya Laraba, ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta fidda bayanin cewa, a shekarar 2020, jarin waje da aka yi amfani da shi a kasar Sin ya kai RMB biliyan 999.98, adadin da ya karu da 6.2%, wanda ya kafa wani sabon matsayi a tarihin kasar Sin.

Yayin da aka fuskanci raguwar zuba jari kai tsaye a cikin kasashen duniya, sakamakon yaduwar cutar COVID-19, kasar Sin ta dukufa matuka domin raya kasuwannin cikin gida wajen janyo masu sha’awar zuba jari. Da farko, Sin ta fito da manufofi don ba da tabbaci ga kamfanonin kasarta domin shimfida zaman karko cikin kasuwannin kasar. Sa’an nan kuma, ta ci gaba da kyautata yanayin harkokin kasuwanci cikin gida, matakan da suka sanya imanin a zukatan kasashen duniya game da kasuwannin kasar Sin.

Haka kuma, tabbacin da kamfanonin kasashen ketare suka nuna wa kasuwannin kasar Sin, ya sa sun samu babbar moriya. Binciken ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya nuna cewa, kaso 60 cikin 100 na kamfanoni masu jarin waje sun samu karin riba a shekarar 2020. Haka kuma, kaso 95 cikin 100 na kamfanonin suna da imani game da makomarsu.

Shekarar 2021, ita ce shekara ta farko da kasar Sin za ta fara aiwatar da shirin “raya kasa na shekaru biyar” karo na 14, kasar Sin wadda ke gaggauta gina sabon salon raya kasa za ta kara bude kofa ga waje, inda za ta gayyaci karin kamfanoni masu jarin waje cikin kasar domin cimma moriyar juna, da samar da damammaki masu kyau ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)