Mata masu saya sana’a na jihar Xinjiang: Aiki na iya kawo girmama da alheri gare mu
2021-01-20 19:27:18 CRI
A wannan zamani da duniya ke fuskantar manyan sauye-sauye, mata masu raya sana’a na ci gaba da koyon dabaru,har su ka kai su ga samun nasarori saboda kokarin su, sun kuma kware a fannoni daban-daban kamar siyasa, tattalin arziki, da al'adu da dai sauransu. Mata ba wai ba su kai maza ba ne a fannin raya sana’a. A cikin shirinmu na yau, za mu baku labarinwasu mata masu raya sana’a da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, wadanda suka kyautata rayuwar iyalansu bisa kokarin da suke yi, tare kuma da taimakawa mutanen dakekewaye da su don su samu wadata tare.
Yayin da aka fara sanyi, lokacin da mazauna a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ke cin gasasshiyar agwagwa a dakin cin abinci, watakila za su iya dandana wani nau’I na abinci Hotan na jihar Xinjiang, mai nisan sama da kilomita 4,000.
Gundumar Luopu da ke yankin Hotan na jihar Xinjiang, tana arewacin tsaunukan Kunlun kuma kusa da kudancin gefen hamadar Taklimakan. Fadin yankin ruwa bai kai kashi 6 cikin 100 na fadin gundumar ba. Don haka, yawancin mazauna wurin, ba su taba ganin agwagwa ba, amma an gina babban sansanin kiwon agwagwi masu salon Beijing 4, wanda girmansa ya kai matsayi na biyu a nan kasar Sin. Agwagwan Beijing 4 wato irin agwagin da ake amfani da su na musamman don gasa gasasshiyar agwagwa na Beijing. Agwagwan da nauyinsu ya wuce ton dubu daya da suka fito daga yankin Hotan sun “tashi”daga gundumar Luopu zuwa manyan birane da larduna na kasar ta Sin, ciki har da Beijing, Shanghai, Zhejiang da dai sauransu.
Wadannan agwagi masu salon Beijing 4, sun fito ne daga kamfanin abinci na Litian Xiangnong da aka kafa a Cibiyar Masana'antu ta Beijing dake gundumar Luopu, kuma kamfanin kiwon agwagwa na Jinxing na birnin Beijing ne ya samar da agwagin da aka kiwata. Daya daga cikin ayyukan rage talauci ta hanyar raya masana'antu na wurin, kamfanin Litian Xangnong ya kafa wasu muhimman sassa a wannan yankin da ya fi fama da talauci a jihar Xinjiang, ciki har da kiwon agwagi, kyankyashe agwagwa, sarrafa abinci, yanka da gyara nama, jigilar kaya da dai sauransu. Ya zuwa yanzu dai,kamfanin yana iya yanka agwagi miliyan 20a ko wace shekara.
A kungiyar masu neman kiwon dabbobi na Fengdou ta kauyen Bostankule dake garin Shanpulu na gundumar Luopu, mun gamu da wata mace mai suna Abbey Maimaiti, yar shekaru 28 a duniya, a yayin da ta waiwayi yadda rayuwar take kafin ta fara aiki a kamfanin, ta ce,
“Kafin na fara aiki a nan, na kan yi aikin noma ne a gida, kudin da nake samu a lokacin, yuan dubu biyu ne kawai a ko wane wata. Amma, bayan da na fara aiki a nan, ina aikin fige gashin agwagi ne, albashina na ako wane wata ya kai 4500, hakika rayuwata ta kyautata sosai.”
Da ma, Abbey Maimaiti ba ta taba fita waje yin aikin ba, in ban da aikin gona da kuma kula da gida.
“Lokacin da na tsaida kudurin soma aiki a wannan kamfanin, duk kan iyalina, ciki har da iyayena, 'yan uwana maza da mata, har da makwabta, sun nuna min goyon baya sosai.”
Abbey Maimaiti ta gayawa wakilanmu cewa, zabin da ta yi na aiki a wannan kamfanin kiwon agwagi, shi ma ya karawa wasu abokanta gwiwar soma aiki a nan. Ta ce,
“Abokaina biyu sun ga albashi yadda albashina ya karu, kuma yanayin rayuwata ta kyautatu. Wadannan sauye-sauye sun sosa musu raisosai, don haka suka yanke shawarar yin aiki a kamfaninmu.”
Bisa kokarin da ta yi, Abbey Maimaiti ta samu Karin girma daga karamar ma’aikaciya zuwa daraktar kula da dakin yin gyare-gyare na kamfanin. Game da buri da fatanta a sabuwar shekara, ta ce,
“Ina fatan, a cikin sabuwar shekara, zan kara kokarin koyon sabbin abubuwa, ta yadda zan kara samun ci gaba a wurin aiki na. A lokaci guda, ina kuma fatan sauran mutane dake wurin, musamman ma 'yan uwanmu Uygur kamar ni, za su yi kokari da kansu, don yi rayuwa mafi kyau.”
Kamfanin Litian Xiangnong yana da ma’aikata guda 570, kuma rabi daga cikinsu, sun taba fama da talauci, kuma rabin ma’aikatan mata ne. Bisa bunkasuwar sana’ar kiwon agwagi a karkashin jagorancin kamfanin, halin da mazauna wurin ke ciki na sauyawa. Abbey Maimaiti ta bayyana cewa,
“Bayan da na fara aiki a wannan kamfanin, ta hanyar kokarin kaina, albashina ya karu sannu a hankali. Bayan na tara isassun kudi, sai na sayi mota, wanda ya saukaka min rayuwa. Bugu da kari, wasu makwabtana ma sun fara aiki a nan, kuma al'ummar mu ta sami babban canje-canje, matsayin mata ma ya inganta sosai a nan.”
“Dan Kudin da na samu sakamakon aikin da nake yi, ya fi kyautar dutsen zinarida sarki zai ba ni. Idan ka inganta rayuwarka da hannunka, wani abin alfahari ne da farin ciki”.
Dilinur Emerniazi, ‘yar shekaru 27 a duniya wadda ke aiki da kungiyar manoma ta gundumar Luopu dake jihar Xinjiang mai cin gashin kai ta Uygur ta kasar Sin tabayyana haka ne ga ‘yan jaridarmu.
Dilinur Emerniazi tana da yara biyu. A 'yan shekarun da suka gabata, ta zauna a gida don kula da yara, yayin ta ga mijinta yana fama da aiki tukuru, ko da yake tana son ita ma ta yi aiki domin ta taimakawa iyalanta kara samun kudin shiga, amma ba ta da damar yin haka. Shekaru biyu da suka gabata, ‘ya’yanta sun tafi makaranta, a don haka ta yanke shawarar fita waje don neman aikin yi.
Saboda tana takardar shaidar kammala karamar digiri na kwaleji kuma ta fahimci fasahar sarrafa kudi, Dilinur Emerniazi ta zama akanta a kungiyar manoma ta garinsu a shekarar da ta gabata, kuma albashinta a wata ya kai RMB yuan 3,500.
“Akwai wani karin magana na kabilar Uygur, wato ‘Dan Kudin da na samu sakamakon aikin da nake gudanarwa, ya fi dutsen kyautar zinarin sarki’. Muna yin aikinmu, muna samun kudinmu,muna kuma rayuwa mai kyau, gaskiya babu wanda yake tilasta mana.”
A watan farko da ta samu albashinta, Dilinur Emerniazi ta yi matukar farin ciki da alfahari. Ta sayawa iyayenta da maijinta sabbin tuffafi, da abinci mai dadi ga yayanta, da kuma sutura da kayan kwalliya ma kanta.
“Wannan kyakkyawar rigar da na sanya, na say nee ta da albashin da na samu,ina farin ciki da alfahari . A da, mijina ne kawai ya ke samun kudi don tallafa wa iyali. Amma yanzu muna da albashi mu biyu, a sakamakon haka, yanayin zaman rayuwar mu ya kyautatu. Yanzu haka, ina kokarin cin jarrabawar samun lasisin tukin mota, kuma ni da miji na muna shirin sayen mota, ta yadda za mu samu saukin zirga-zirga da ma kai yaran mu wajen wasanni da nishadi.”
sakamakon maganganun da wasu hukumomin kasashen waje suka yi game da “tilastawa mata yin aiki a Xinjiang” da “yin aiki ala tilas”,Dilinur Emerniazi ta kyama ci wannan batu sosai. Ta ce a wannan shekarar da muke ciki tana shirin koyon ilimin gudanarwa, tare da kara samu kwarewa a wasu fannoni, don kara taka muhimmiyar rawa a wajen aiki.
“Ina so in tambayi wadannan mutanen kasashen ketare masu boyayyiyar manufa, wai shin daidai ba ne mu samu kyakkyawar rayuwa da kan mu? Bai kamata Mata su fita aiki ba? Idan bamu fita aiki ba, zaku bamu kudi? Ko kuma za ku taimaka mana wajen ciyar da yaranmu?”
Kelly Binur Kurban matashiya ce daga garin Turpan. Koda yake ba ta tsufa ba, ita ce shugabar wani kamfani na sakar dardumar hannu, tana kula da ma'aikata sama da 70, kuma darajar kayayyakin da kamfaninta ya fitar a ko wace shekara ta kai fiye da yuan miliyan 15.
Ta ce da farko, iyayenta sun bude wani shagon sayar da darduma, mahaifinta ya kan sayi kaya daga Hotan, mai nisan kilomita dubu biyu, gaskiya a lokacin ya kan yi tafiya mai nisa kuma ya kan yi aiki tukuru. Daga baya, ta tattauna da mahaifinta don bude wata masana'antar saka a Turpan, don ta gaji tsohuwar fasarar gargajiya ta saka darduma da hannu irin ta kabilar Uygur. A bisa taimakon gwamnatin wurin a fannonin tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu, da ba da rangwamen rance, da kuma samar da kwarewa, ya taimakawa iyayenta yin odar na’urorin saka kaya da hannu guda 80, hakan ya bas u damar gina layin gyaran katifu na zamani, da daukar ma'aikata 70 masu fasahar saka, ta yadda ake iya fitar da katifu da aka saka da hannu da suka kai murabba'i 1,500, da kayan yadi guda 38,000 a kowace shekara, inda kudaden shigar da kamfanin ke samu a duk shekara ya kai yuan miliyan 15.
Kelly Binur Kurban ta ce, kwadago hakkin kowane dan kasa ne. yadda mata ke raya sana’a, ya dace da halin da ake ciki a yanzu, kuma aikin kwadago na kawo mana daukaka da alheri.
“Za mu ci gaba da aiki tukuru a nan gaba, don raya fasahar saka katifun kabilarmu da ake yi da hannu, da kuma tufaffi da kayanmu na ado, za kuma mu kara kokari, ta yadda a nan gaba kayan kamfaninmu ya shiga lungu da sakon kasar Sin da ma duniya baki. Ban da wannan kuma, za mu kara himma don kara samar da ayyukan yi da kara taimakawa sauran mutane don su samu wadata.”