logo

HAUSA

Lawal Saleh: Ziyarar ministan harkokin wajen Sin a Afirka tana da babbar ma’ana

2021-01-19 14:27:11 CRI

Lawal Saleh: Ziyarar ministan harkokin wajen Sin a Afirka tana da babbar ma’ana_fororder_微信图片_20210117211127

A kwanan nan wato daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Janairu, memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Mista Wang Yi ya ziyarci wasu kasashen Afirka biyar, wadanda suka hada da Najeriya, da Jamhuryar Demokuradiyyar Kongo, da Botswana, da Tanzaniya da kuma Seychelles. A daidai lokacin da annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya, ziyarar minista Wang a Afirka ta shaida irin dadadden zumunci da kyakkyawar alaka dake tsakanin bangarorin biyu.

Menene ainihin makasudin ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a kasashen Afirka a bana? Ta yaya al’ummar Najeriya za su ci alfanu daga irin wannan kyakkyawar huldar dake tsakanin kasar Sin da Najeriya? Yaya kasashen biyu za su karfafa hadin-gwiwa domin yakar annobar COVID-19? Domin samun amsar wadannan tambayoyi masu jawo hankali, Murtala Zhang ya zanta da shahararren mai sharhi kan harkokin yau da kullum da kuma dangantakar kasa da kasa, malam Lawal Saleh a Abuja. (Murtala Zhang)