logo

HAUSA

Karuwar tattalin arzikin Sin wanda ya wuce tsammani yana taimakawa farfadowar harkokin duk duniya

2021-01-18 21:33:55 CRI

Karuwar tattalin arzikin Sin wanda ya wuce tsammani yana taimakawa farfadowar harkokin duk duniya_fororder_A

Yau Litinin, gwamnatin kasar Sin ta bullo da wasu alkaluman kididdiga kan tattalin arzikin kasar a shekarar da ta gabata, inda aka nuna cewa, yawan GDPn kasar ya zarce Yuan triliyan 100, wanda ya kai Yuan triliyan 101.6, adadin da ya karu da kaso 2.3 idan aka kwatanta da na shekara ta 2019. Kafofin watsa labaran kasa da kasa sun bayyana cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya wuce hasashen da aka yi.

Yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa, kana tattalin arzikin duniya ke samun koma-baya sosai, tattalin arzikin kasar Sin ya samu farfadowa yadda ya kamata, har ma za ta kasance muhimmiyar kasa daya tak a duniya, wadda za ta samu karuwar tattalin arziki. Wannan abu yana da muhimmancin gaske ga duk duniya, saboda karuwar tattalin arzikin Sin yana taimakawa farfadowar tattalin arzikin duk duniya.

Karuwar tattalin arzikin Sin wanda ya wuce tsammani yana taimakawa farfadowar harkokin duk duniya_fororder_B

A farkon watan Janairun bana, bankin duniya ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya ya ragu da kaso 4.3 a shekara ta 2020. Amma ina dalilin da ya sa tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasa kamar haka? Dalilin dai shi ne, kasar Sin ta dinga yin kirkire-kirkire, da kuma maida hankali kan raya kasuwa. Kasar Sin tana da dimbin al’umma da yawansu ya kai biliyan 1.4, irin wannan babbar kasuwa ta taimaka mata wajen shawo kan hadurran da za su kunno kai.

Bugu da kari, a shekara ta 2020, cinikin da aka yi ta kafar sadarwar intanet a kasar Sin ya zarce Yuan triliyan 11.76, adadin da ya karu da kaso 10.9 idan aka kwatanta da na shekara ta 2019, kuma tattalin arzikin da aka raya ta kafar sadarwar intanet, ya taimaka sosai ga farfadowar kasuwar saye da sayarwa ta kasar.

Har wa yau, gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da wasu kyawawan matakai, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da guraban ayyukan yi, da kyautata rayuwar al’umma da sauransu.

Karuwar tattalin arzikin Sin wanda ya wuce tsammani yana taimakawa farfadowar harkokin duk duniya_fororder_C

A yayin da ake kokarin dunkule tattalin arzikin duniya baki daya, babu wata kasa ko wani mutum, wanda zai iya raba kansa daga saura, a fannin tinkarar hadurra gami da kalubaloli daban-daban. Kasar Sin ta fahimci haka sosai, har ma ta rabawa duk duniya dabararta, wato gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya don samun moriya tare.

Tattalin arzikin kasar Sin ya samu dimbin nasarori a shekara ta 2020, al’amarin da ya aza tubali mai inganci ga bude wani sabo babi na neman ci gaba. Amma har yanzu akwai rashin sanin tabbas game da canjin annobar COVID-19, shi ma farfadowar tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar irin wannan matsala. Don haka kasar Sin za ta fara aiwatar da shirinta na raya kasa na shekaru biyar karo na 14 yadda ya kamata, don kara samar da damammaki ga sauran kasashe.

Kamar yadda wani kwararre kan harkokin kasar Sin daga kasar Mexico ya ce, a matsayinta na wata babbar kasa da ta taimaka ga ci gaban tattalin arzikin duniya, Sin za ta ci gaba da bada gudummawarta ga farfadowar tattalin arzikin duk duniya baki daya.(Murtala Zhang)