logo

HAUSA

Amurka za ta yi wa kanta illa, idan ta ci gaba da hana hajojin jihar Xinjiang shiga kasar

2021-01-16 17:41:04 CRI

Amurka za ta yi wa kanta illa, idan ta ci gaba da hana hajojin jihar Xinjiang shiga kasar_fororder_hoto

A kwanan nan, hukumar kwastan da hukumar kare iyakokin Amurka, sun sanar da cewa, za su tsare auduga da tumatir da wasu kayayyakin jihar Xinjiang ta kasar Sin a tashoshin shiga kasar. Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na ABC na Amurka ya ruwaito, cikin shekarar 2020, hukumar kwastan ta Amurka ta fidda umurnin tsare hajoji 13, kuma 8 daga cikinsu hajoji ne na jihar Xinjiang.

A matsayinsu na manyan sana’o’in jihar Xinjiang, samar da auduga da tumatir, sun kirkiro guraben aikin yi masu yawa ga al’ummomin jihar. ‘Yan siyasar Amurka su kan kira kansu da masu rajin kare hakkin bil Adama, amma, a hakika, suna daukar matakan da za su haddasa rashin aikin yi a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

’Yan siyasar kasar Amurka suna son amfani da batun jihar Xinjiang domin hana ci gaban kasar Sin, shi ya sa, kasar ta ba da umurnin tsare hajojin jihar. Amma, gabanin yanayin dunkulewar kasa da kasa, matakin zai haifar da illa ga kamfanonin Amurka.

Alal misali, jihar Xinjiang ta kasar Sin wurin ne da ya fi samar da auduga ga kasashen duniya, umurnin tsare audugan jihar Xinjiang da Amurka ta bayar, zai haddasa matsala ga kamfanonin dake da alaka da auduga, sa’an nan, zai yi mummunan tasiri ga kasuwannin duniya, lamarin zai harzuka al’ummomin Amurka.

Manazarta na ganin cewa, kusan dukkanin kamfanonin tufafi na kasa da kasa suna amfani da audugar jihar Xinjiang, kana, bisa umurnin da gwamnatin Amurka ta bayar, wadannan kamfanoni za su gamu da matsala, wadda za ta yi barazana ga tsarin samar da kayayyaki cikin kasa da kasa, da yi wa yanayin farfadowar tattalin arzikin duniya tarnaki.

A maimakon mai da hankali kan warware matsalolin da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta haddasa wa kasarsu, wasu ‘yan siyasar Amurka na amfani da batun jihar Xinjiang domin kawo tashe-tashen hankula, da bata moriyar kasa da kasa, lamarin da ba makawa, zai musu illa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)