logo

HAUSA

Bangarori masu samar da taimakon kudi ga ‘yan siyasa na lalata yanayin siyasar Amurka

2021-01-16 20:06:51 CRI

Bangarori masu samar da taimakon kudi ga ‘yan siyasa na lalata yanayin siyasar Amurka_fororder_210116-sharhi-maryam2-hoto

A kasar Amurka, bangarori masu samar da kudi ga ‘yan siyasa da bangarorin siyasa suna cikin hadin gwiwa mai zurfi, kuma bangarori masu samar da taimakon kudi ga ‘yan siyasa su kan ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasa, lamarin dake ci gaba da bata yanayin siyasa a kasar Amurka.

A kasar Amurka, bangarori masu samar da kudi ga ‘yan siyasa da wasu mutane su kan yi tasiri kan manufofin gwamnati. Bisa kididdigar da kungiyar Opensecrets ta kasar Amurka ta fidda, daga shekarar 2000 zuwa shekarar 2019, adadin masu ba da shawara ga ‘yan siyasa da suka yi rajista ya kai dubu 10 cikin ko wace shekara. Kuma, bisa wasu shawarwarin da suke ba ‘yan siyasar kasar, a kan sanya moriyar manyan kamfanoni a gaban moriyar jama’a, sabo da wasu al’ummomin ba su san yadda za su bada shawara ga ‘yan siyasa ba, hakan ya sa, gwamnatin kasar ta kasa mai da hankali kan bukatunsu.

Abun takaici shi ne, bangarori masu samar da taimakon kudi ga ‘yan siyasa suna babban tasiri kan zaben shugaban kasar Amurka, bisa dimbin kudaden da suka tattara da samar wa ‘yan takara. Bayan wani dan siyasa ya kama aikin shugaban kasa kuma, tabbas ne ya samar da wasu manufofi domin goyon bayan bangarorin da suka taba samar masa taimakon kudi.

Kamar gwamnatin Amurka ta yanzu, tana da dangantakar abota mai kyau da kamfanonin hada-hadar kudi na Wall Street, ministan harkokin kudin kasar Steven Mnuchin ya taba aiki a kamfanonin Goldman Sachs da kamfanin asusun Soros, kana, tsohon mai ba da shawarar tattalin arziki na fadar White House Gary Cohn, ya taba zama shugaban kamfanin Goldman Sachs, a kan kira wadannan mutanen biyu da bangaren Goldman Sachs dake cikin gwamnatin kasar Amurka.

Lamarin da ya nuna cewa, harkokin kudi suna ba da tasiri mai zurfi kan siyasar kasar Amurka, kuma, babu wani shugaban kasar da zai iya canja wannan lamari. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)