logo

HAUSA

Allurar rigakafin da Sin ta samar na da inganci

2021-01-15 16:21:17 CRI

Allurar rigakafin da Sin ta samar na da inganci_fororder_001WLsZ7ly1gjvubqfyaoj60pu0h6js902

Ran 30 ga watan Disamba na shekarar bara, bayan allurar rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar ya samu iznin shiga kasuwa a UAE da Bahrain, yanzu haka ya kara samun izinin shiga kasuwar kasar Sin. Kafin wannan kuma, an yi amfani da wannan allura cikin gaggawa a kasar Sin, da UAE da Bahrain da Masar da Jordan.

Ban da wannan kuma, an yi wa shugabanni da kusoshin kasashe 10 wannan allura. Har wa yau, kasashe fiye da 50 suna bukatar sayen wannan allura.

Abin da ya fi jawo hankalin jama’a shi ne ingancin allurar da aka samar. Ma’aunin kimanta ingancin wata allura shi ne lura da cewa ko za ta haifar da matsala, da karfinta na yin rigakafi, da farashin sayar da ita. To, bari mu ga wasu hakikanin gaske game da allurar da Sin ta samar.

Na farko, wannan allurar da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar, an yi mata gwaji bisa matakai uku, a matakin farko da na biyu an yi gwaji kan mutane da suke da shekaru 18 zuwa 59 da haifuwa, a mataki na 3 kuma, an yi gwajin ta kan mutane dake da shekaru 3-17 da haifuwa. Duk aikin gwaji da aka yi bai haifar da wata babbar matsala ba. Ko wata allurar da kamfanin ya samar ana iya bin sahunta a kan Intanet, tun daga lokacin da aka samar da ita, da hanyoyin da ake sufurinta, da lura da wadanda aka yi masa wannan allura.

A cikin kasar Sin, an yi wa mutanen da yawansu ya kai miliyan 1 wannan allura a birnin Beijing, inda a birnin Shanghai wannan adadi ya kai dubu 602, kana yawan allurar da aka yi amfani da su a kasar Sin ya kai fiye da miliyan 10.

Na biyu, wannan allurar da aka samar da ita ba da dadewa ba, duk da cewa ana gudanar da aikin gwaji sau da dama, don kokarin ba da tabbacin ba ta haifar da babbar matsala, amma za a gano karfinta na yin rigakafi cikin dogon lokaci. Babu wata allura da aka samar a cikin tarihi da ake da tabbacin cewa, tana da amfani matuka kan Bil Adama tun daga farko. Ana kuma yin aikin gwaji sau da dama a kan wasu dabbobi don kimanta amfaninta.

Na uku, kamfanin Sinopharm ya kafa sansaninsa biyu a birnin Beijing, da Shanghai, don samar da allurar, inda ya zuwa karshen shekarar bara, yawan allurar da ya samar ya kai kimanin miliyan 100. An kuma yi kiyasin cewa, wannan adadi zai kai biliyan 1 a shekarar bana, wadanda ake iya sufurinsu cikin motar dakon kayayyaki dake bukatar sanyi, kuma yawancin kasashe na da wannan fasahar surufi, abin da ya rage farashin sufurin allurar a duniya. Ban da wannan kuma, kasar Sin na kokarin rarraba fasahohinta na samar da allurar ga kasashen duniya, da hadin kanta da sauran kasashe wajen yakar cutar, musamman ma kasashe maso tasowa, ta yadda jama’ar wadannan kasashe za su samu alluran ba tare da kashe kudade da yawa ba. (Amina Xu)