logo

HAUSA

Kara gudanar da ayyuka masu amfani don raya hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

2021-01-15 14:49:32 CRI

A farkon shekarar 2021, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ci gaba da bin manufar zabar nahiyar Afirka a matsayin ziyara ta farko ta ministan harkokin wajen Sin, wadda aka kiyaye ta har na tsawon shekaru fiye da 30, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta sake jawo hankalin kasa da kasa.

Domin samun moriyarsu, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun zargi hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, domin lalace huldar dake tsakaninsu. Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya taba bayyana cewa, kasar Amurka ta samar da gudummawa ga kasashen Afirka, domin Amurka ta maida ita a matsayin manufa mai dacewa, amma Sin ta samar da gudummawa ga kasashen Afirka domin samun moriya daga nahiyar.

Game da yadda ake yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, jama’ar Afirka sun fi kowa sanin amsar batun.

A shekarar 2020, ban da yaduwar cutar COVID-19, kasashen Afirka da dama sun yi fama da bala’in fari, gwamnatin kasar Sin ta samar wa kasashen kamar su Uganda da sauransu, da maganin kashe fari da na’urorin zuba maganin, kana an samar musu da rigunan ba da kariya da abin rufe baki da hanci da kuma safar hannu.

Ministan harkokin aikin noma da kiwon dabbobi da kamun kifi na kasar Uganda Vincent Bamulangaki Sempijja ya bayyana cewa, wadannan kayayyaki suna samar da babbar gudummawa ga kiyaye tsaron abinci na jama’ar kasar Uganda.

Kana Sin tana rika samar da fasahohin zamani ga kasashen Afirka, wasu kamfanonin aikin noma na kasar Sin da hukumomin nazari sun gudanar da shirye-shiryen yin shuke-shuke a wasu yankunan Afirka, wata mace mai sana’ar noma ta kasar Mozambique mai suna Joanna, wadda ta karba gudummawar ta bayyana cewa, a da hatsin da ta shuka yana biyan bukatun gidanta ne kawai, amma bayan da ta shiga shirye-shiryen yin shuke-shuke na hadin gwiwa, ta kara samun kudin shiga, har ta iya kai yaran ta zuwa makaranta, da kara saya musu sabbin riguna, da kuma sayen sabon firiji.

Kafin wannan, ba su taba tunanin irin wannan babban sauyin da ya faru ba.

Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, bisa bukatun jama’ar Afirka, don haka ya kamata a kara gudanar da ayyuka masu amfani don raya hadin gwiwarsu.

Ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta gina hanyoyin jiragen kasa masu tsawon fiye da kilomita dubu shida, da hanyoyin motoci masu tsawon fiye da kilomita dubu shida, da tashoshin ruwan teku kimanin 20, da manyan na’urorin samar da wutar lantarki fiye da 80, da asibitoci fiye da 130, da dakunan wasannin motsa jiki 45, da kuma makarantu fiye da 170 a kasashen Afirka. Kana Sin ta tura wa kasashen Afirka 48 ma’aikatan kiwon lafiya dubu 21, wadanda suka ba da jinya ga marasa lafiya na Afirka kimanin miliyan 220. An yi hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a wurare daban daban na Afirka, wanda ya biya bukatun Afirka da kuma kyautata zaman rayuwar jama’ar Afirka. Gaskiya daya ce, daga kinta sai bata.

Sin tana samar da gudummawa, da goyon baya, da kuma hadin gwiwa ga nahiyar Afirka bisa bukatu da moriyar Afirka, da girmama Afirka da saurara ra’ayoyin Afirka. Sin ta yi hakan ne ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba, ba kuma tare da tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasashen Afirka ba.

Bisa hasashen samun moriyar juna ta hadin gwiwa, a farkon bana, kasashen Congo Kinshasa da Botswana, sun daddale takardar fahimtar juna kan shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da kasar Sin, inda suka zama kasashe na 45 da 46, da suka shiga hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”.

A nan gaba, Sin da Afirka za su gudanar da shirye-shiryen raya sana’ar kere kere, da aikin noma, da sadarwa a nahiyar Afirka, za a yi amfani da fasahohi da kwarewar Sin a wadannan fannoni, don taimakawa Afirka wajen fadada kasuwar kasar Sin, da inganta karfinsu na samun ci gaba, da kuma kara kudin shiga na jama’arsu.

Sin ta yi bayani sau da dama cewa ba ta yaki da kowa. Kuma hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka bai rufe kofa ga wani sashe na duniya ba, kaza lika Sin ta yi maraba da kasa da kasa, da su kara zuba jari ga Afirka don samun ci gaba tare. (Zainab)