logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta gaggauta dakatar da salon nuna danniya

2021-01-14 19:26:31 CRI

Ya kamata Amurka ta gaggauta dakatar da salon nuna danniya_fororder_微信图片_20210114191932

A farkon wannan mako da muke ciki ne mahukuntan Amurka, suka fitar da wani rahoton aiki, mai kunshe da manufofin kasar game da dangantakar ta da kasar Indiya, da kasashen dake kewayen tekun Fasifik, inda a ciki, Washington ta bayyana kin jinin ta ga kasar Sin, tare da fatan aiwatar da wasu matakai na gurgunta zaman lafiya da daidaito a yankin.

Ko da yake, kowace kasa na da ikon kulla huldar diflomasiyya tsakaninta da sauran sassan duniya, amma a hannu guda, bayyana Indiya a matsayin kasa da Amurka ke fatan dagawarta zai rinjayi kasar Sin a wannan yanki, ya sabawa tsarin takara cikin lumana, kuma hakan nuna wariya ne ga kasar Sin.

A hannu guda, wancan rahoto ya nuna karara, yadda Amurka ke alkawarta baiwa yankin Taiwan kariya daga duk wani hari da yankin ka iya fuskanta, tare da nuna cewa, wai Amurkar za ta dauwamar da tasirin ta a yankin.

Dukkanin wadannan kalamai da alkawura na Amurka, suna nuni ne ga abubuwa da ba za su haifar da da mai ido ba. Amurka tana yiwa kawayen ta na kewayen tekun Fasifik romon baka, cewa za ta kare su, duk kuwa da cewa ba sa fuskantar wata barazana. A lokaci guda, tana zuga kasashen dake da kusanci, su yi watsi da hadin kansu, su kuma rika ganin baiken juna, da yin takara maras tsafta. Amurka na nuna iko na aiwatar da mulkin mulaka’u, ko salon danniya ga kasashen da take dauka a matsayin abokan gabar ta.

Tuni dai mahukuntan Sin suka bayyana aniyar Amurka, a matsayin wata makarkashiya ta wargaza manufar kasar Sin, ta kyautata dangantaka da makwaftanta, da rura wutar rashin jituwa, tare da yayata farfagandar nan ta cewa, wai Sin barazana ce ga sauran kasashe, duk kuwa da cewa, Amurkar ba ta iya gabatar da wata shaida mai gamsarwa kan hakan.

To sai dai kuma, a fili take cewa, kasar Sin ta sha aiwatar da manufofi, da matakan tabbatar da zaman lafiya da daidaito, da ci gaba tsakanin ta da makwaftan ta na wannan yanki, sabanin Amurka da har kullum, tarihin ta ke cike da rura wutar yake yake, da yiwa hadin kai da zaman lafiyar yankunan duniya kafar ungulu.

Ko shakka babu, tarihi ba zai taba mantawa da gudumawar masu neman wanzar da zaman lafiya da lumana ba, kana ba zai yafewa masu fatan ganin sun yi danniya, da nuna karfin tuwo kan sauran sassan kasa da kasa ba!!! (Saminu Hassan)

Bello