Ministan wajen Sin ya kammala ziyarar da ya kai Afirka a shekarar 2021
2021-01-13 09:40:07 CRI
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar sada zumunta da duk wani ministan wajen kasar Sin ke kaiwa a farkon kowace sabuwar shekara zuwa kasashen Afirka, inda a wannan karo ministan ya ziyarci kasashen Afirka biyar da suka hada da Najeriya, da Tanzaniya, da Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) da Botswana da Seychelles.
Duk da annobar COVID-19 da ke ci gaba da addabar sassan duniya, ba ta hana ministan na kasar Sin kai wannan ziyara ba. Wang Yi ya ce, taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, na shekarar 2018, ya cimma nasarori, kuma ya zama sabon kuzari ga dangantakar abota dake tsakanin bangarorin biyu.
Haka kuma, kasar Sin ta tabbatar da aiwatar da manyan shirye-shirye 8 da aka gabatar yayin taron kolin da aka yi a Beijing.
Ministan ya kuma gabatar da wasu bangarori 7 na daukaka dangantakar bangarorin biyu zuwa wani sabon mataki, baya ga albishir din da ministan ya gabatar a kowace kasa da ya ziyarta, da suka hada da batun yaki da wannan annoba ta COVID-19, da samar da kayayyakin more rayuwa, da gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, da goyon bayan Afirka a fannin fada a ji a harkokin kasa da kasa, da ci gaba da yayata manufar cudanyar sassa daban-daban da makamatansu.
A cewarsa, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya da nahiyar Afrika, da nufin ganin bayan annobar COVID-19 baki daya, da bunkasa karfin samar da kayayyaki. Wato za ta taimakawa nahiyar kara karfinta, domin dogaro da kanta wajen samar da kayayyaki kirar Afrika
Bugu da kari, kasar Sin za ta kara hade kasashen nahiyar ta fuskar ababen more rayuwa, da hadin gwiwar ciniki cikin ’yanci a tsakaninsu, da kare moriyar kasashe masu tasowa.
Kasar Sin za ta inganta hadin gwiwarsu a bangaren aikin gona, ta yadda nahiyar Afrika za ta zama mai wadatar amfanin gona, da karfafa hadin gwiwarsu a bangaren fasahohin zamani, domin samar da nahiyar Afrika mai tafiyar da zamani. Da kara yin hadin gwiwa a bangaren kare muhalli. Haka kuma sassan biyu, wato Sin da Afirka, za su karfafa hadin gwiwa a fannin aikin soja, domin tabbatar da tsaro a nahiyar Afirka.
Tun a shekarar 1991, kasar Sin take gudanar da wannan al’ada ta fara ziyartar aminansu na kasashen Afirka, abin dake kara nuna irin dankon zumuncin dake tsakanin bangarorin biyu. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)