Mustapha Bala Tsakuwa wanda ya bada gudummawa a fannin fadakar da al’umma kan yakar cutar COVID-19
2021-01-12 14:31:30 CRI
Dakta Mustapha Bala Tsakuwa, mai nazari da kuma bincike ne a kan koyo da kuma koyar da harshen Turanci a jami’ar da ake kira jami’ar kudu-maso-yamma wato Southwest University, wacce take a gundumar Beibei dake birnin Chongqing a kasar Sin.
A yayin hirar da ya yi da Murtala Zhang, malam Tsakuwa ya yi tsokaci kan karatu gami da nazarin da yake yi a kasar Sin, da kuma rayuwarsa ta yau da kullum a kasar. Ya kuma bayyana ra’ayinsa kan kokarin da gwamnatin kasar take yi, a fannin dakile yaduwar annobar COVID-19, inda ya ce, shi ma ya bada tasa gudummawa wajen yakar cutar a kasar Sin da ma gida Najeriya.(Murtala Zhang)