logo

HAUSA

'Yancin bayyana ra'ayi na kasar Amurka abu ne mai ban mamaki

2021-01-11 20:35:56 CRI

'Yancin bayyana ra'ayi na kasar Amurka abu ne mai ban mamaki_fororder_20210111-Amurka-sharhi-Bello

Shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump, ya gamu da wani abun kunya a kwanakin nan, ganin yadda wasu shafukan sada zumunta na kasar Amurka suka toshe shafunkansa, bisa dalilin kokarin rura wutar ta da rikici a kasar. Sai dai babban abin kunya shi ne, a kasar Amurka da kullum take kambama kanta cewa tana da “yanci na bayyana ra'ayi”, an hana shugaban kasar ‘yancin yin magana a shafin sada zumunta.

Wasu na cewa, shugaba Trump ya wallafa kalmomin rura wutar rikici a shafin, lamarin da ya keta dokokin amfani da shafukan sada zumunta, don haka ya kamata a toshe shafin da ya saba amfani da shi yana kalaman da ya ga dama. Wannan batu haka yake, domin ya kamata a daina aikata abubuwan da za su ta da rikici a shafukan sada zumunta. Sai dai tambaya a nan ita ce: a shekaru 4 da suka wuce, Shugaba Trump ya yi ta wallafa maganganun da ba su dace ba a shafukan sada zumunta, cikinsu akwai yada labarai na jabu, da rurura wutar kiyaya da rikici. Amma me ya sa shafukan sada zumunta na kasar Amurka ba su yi kome ba sai a yanzu?

Jaridar Washington Post ta kasar Amurka ta ce, ya zuwa watan Mayun bara, Shugaba Donald Trump ya wallafa kalaman jabu fiye da dubu 18 a shafukan sada zumunta, kana wasu fiye da 3300 daga cikinsu ya watsa su ne kan shafin Twitter.

Idan aka yi la’akari da lokacin da wadannan abubuwa suka abku, za a fahimci cewa, yadda kafofin sada zumunta na kasar Amurka, sun hana shugaban kasarsu magana, tamkar wani mataki ne na hana rura wutar rikici, amma a hakika sun dauki matakin ne bisa son rai da neman tabbatar da moriyar siyasa. Hakan ya nuna cewa, ko da yake kasar Amurka ta kan yi takama cewa, tana da ‘yanci na bayyana ra’ayi, amma a hakika ana yin amfani da wannan “’yanci” ne wajen neman biyan bukata a fannin siyasa. (Bello Wang)

Bello