logo

HAUSA

Za a kara hadin gwiwa wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka

2021-01-11 11:47:53 CRI

Za a kara hadin gwiwa wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka_fororder_20210111-rahoto-Sanusi Chen-hoto2

A tsakanin ranakun 4 da 9 ga wata, dan majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyara kasashen Afirka biyar, da suka hada da Najeriya da Congo Kinshasa da Botswana da Tanzaniya da Seychelles. Bayan ya kammala ziyararsa a Afirka, Mr. Wang Yi ya zanta da wakilan kasar Sin game da sakamakon da ya samu a ziyarar. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, kowanne ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan kaddamar da ziyararsa ta farko a kowace shekara a wasu kasashen Afirka. Ko da yake a bana, akwai yaduwar annobar COVID-19 a duk fadin duniya, amma bangaren Sin bai canja wannan al’ada ba, inda ya yi niyyar ci gaba da raya ta. Kasashen Afirka ma suna maraba da zuwan abokai daga kasar Sin, bangarorin Sin da Afrika na bukatar tattaunawa da kuma shawo kan wasu matsaloli masu tsanani da suke fuskanta tare, ta hanyar ganawa fuska da fuska, ta yadda za su iya samun sabbin damammakin kara hadin gwiwa domin samun wata kyakkyawar makoma mai haske kwarai.

Za a kara hadin gwiwa wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka_fororder_20210111-rahoto-Sanusi Chen-hoto3

A lokacin da Wang Yi yake ziyara a kasashen Afirka biyar, abokan Afirka sun yi maraba da zuwansa da hannu bibbiyu, inda shugabanni da ministocin harkokin wajen wadannan kasashe, dukkansu suka gana da shi tare da tattaunawa kan yadda za a tabbatar da aiwatar da muhimmin matsayar da shugabannin Sin da Afirka suka cimma, da karfafa zumuncin gargajiya dake kasancewa tsakanin Sin da Afirka, da batun amincewa da juna a fannin siyasa da kuma batun tinkarar annobar COVID-19 cikin hadin gwiwa, da batun farfardo da aikin hanzarta gina wasu muhimman ayyuka, da kuma ingiza tafiyar da shawarar “ziri daya da hanya daya” da dai sauran muhimman batutuwa, har ma sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama.

Har yanzu annobar COVID-19 tana yaduwa a karo na biyu a duk fadin duniya. Bangaren Sin zai ci gaba da samar da kayayyakin kandagarkin annobar, da tura tawagogin jami’an jinya zuwa kasashen Afirka masu bukata, da kuma kara hadin gwiwa tsakanin asibitocin kasar Sin da na kasashen Afirka, ta yadda za su iya musayar fasahohin tinkarar annobar kai tsaye. Bugu da kari, za a hanzarta gina hedkwatar cibiyar Afirka-CDC, da kuma hadin gwiwar sauran kasashen G20 wajen tafiyar da aikin sassauta basusukan da kasashen Afirka suka ci. Sannan kuma kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da wasu kasashen Afirka a fannin nazari da kuma samar da allurar rigakafin annobar, ta yadda za a iya tabbatar da ganin kasashen Afirka sun samu allurar kamar yadda ake fatan.

A yayin da ake kokarin shawo kan annobar, yadda za a iya tafiyar da tattalin arziki da kuma ba da tabbaci ga zaman rayuwar al’umma, suna da muhimmanci sosai. Har yanzu bangaren Sin yana gudanar da ayyuka fiye da 1100 a kasashen Afirka, wadanda shi da bangarorin Afirka suka kafa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”. Injiniyoyin kasar Sin kusan dubu 100 har yanzu suna tsayawa kan ayyukansu a Afirka. An kuma farfado da gina wasu ayyukan shimfida layin dogo da hanyoyin mota da tasoshin samar da wuta mai aiki da makamashin ruwa. Wadannan ayyuka sun bayar da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da zaman takewar kasashen Afirka.

Za a kara hadin gwiwa wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka_fororder_20210111-rahoto-Sanusi Chen-hoto1

A lokacin da yake tabo maganar aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” a Afirka, Wang Yi ya ce, a lokacin da ya ziyarci kasashen Congo Kinshasa da Botswana, Sin da kasashen, sun rattaba hannu kan takardar fahimtar juna kan shawarar “ziri daya da hanya daya”. Sakamakon haka, wadannan kasashen biyu sun zama kasashe abokai na 45 da na 46 wajen tafiyar da shawarar “ziri daya da hanya daya” a Afirka.

A bana ake cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC. Ana kuma shirin shirya wani taron FOCAC a bana. Wang Yi ya bayyana cewa, a lokacin da ya ziyarci kasashen Afirka, ya kuma saurari ra’ayoyin abokan Afirka kan yadda za a iya shirya wannan taro kamar yadda ake fata. Dukkansu sun bayyana cewa, ya kamata a kara hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin a fannonin kiwon lafiya da samar da kayayyaki da kara tuntubar juna tsakanin shiyya-shiyya, da aikin gona da amfani da bayanan kwafuta na zamani da kare muhalli da aikin soja da kuma batun horar da kwararru da dai makamatansu, domin taimakawa kara ci gaban kasashen Afirka. (Sanusi Chen)