logo

HAUSA

Wane ne abokin kasashen Afirka na gaske?

2021-01-11 20:59:15 CRI

Wane ne abokin kasashen Afirka na gaske?_fororder_20210111-sin-afirka-sharhi-Bello

Har yanzu muna tuna wata maganar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada, a wani taron koli na musamman da aka kira watanni 6 da suka wuce, don karfafa hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka a bangaren tinkarar cutar COVID-19, inda shugaban ya ce, “ Duk wani sauyin da za a samu a duniya, kasar Sin ba za ta taba yin watsi da niyyarta ta kokarin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka ba.” Ban da haka, shugaban ya jaddada wajibcin hadin gwiwa da juna a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannin tinkarar cutar COVID-19. Daga bisani, a farkon bana, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya ziyarci wasu kasashe 5 dake nahiyar Afirka, da suka hada da Najeriya, da Kongo Kinshasa, da Botswana, da Tanzania, da Seychelles, tare da samun nasarori sosai, abun da ya shaida yadda kasar Sin take kokarin cika alkawarinta na karfafa hulda tare da kasashen Afirka.

Yadda ake tura manyan jami’ai don ziyartar kasashen Afirka a farkon ko wace sabuwar shekara, wata dadaddiyar al’ada ce, da kasar Sin take kokarin aiwatar kusan shekaru 31 a jere. Duk da cewa, yanzu haka ana fama da annobar COVID-19 a kasashe daban daban, amma wannan bai sa kasar ta dakatar da wannan nagartacciyar al’ada ba. Wannan ya nuna cewa, kasar Sin na da sahihanci sosai a fannin neman hadin gwiwa tare da kasashen Afirka don tinkarar matsalolin da ake fuskanta tare. Cikin wadannan kwanaki 5 da minista Wang Yi ya shafe yana ziyara a nahiyar Afirka, jami’an Sin da Afirka sun cimma daidaito sosai, a fannonin tinkarar cutar COVID-19, da farfado da manyan ayyuka na hadin gwiwa, da ci gaba da raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da karfafa mu’amalarsu kan wasu batutuwan kasa da kasa da na shiyyoyi daban daban, inda bangarorin Sin da Afirka, suka kulla yarjeniyoyi daban daban, tare da sheda cikakkiyar damar samun ci gaba a kokarin karfafa huldar hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Wani salon musamman game da huldar dake tsakanin Sin da Afirka, shi ne yadda suke kokarin taimakon juna a lokacin da suke fuskantar matsala. A shekarar 2020 da ta wuce, kasar Sin da kasashen Afirka sun yi kokarin taimakawa juna don dakile cutar COVID-19, lamarin da ya zama abin koyi ga sauran kasashe daban daban. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hira da takwarorinsa na kasashen Afirka ta wayar tarho har sau da dama, tare da kiran bude taron koli na hadin gwiwar Sin da Afirka don tinkarar annoba, inda shi da shugabannin kasashen Afirka suka ba da muhimmin jagoranci ga aikin dakile cutar COVID-19 bisa hadin gwiwar Sin da Afirka. Daga bisani kasar Sin ta samar da dauki ga kasashe 53 dake nahiyar Afirka, gami da kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU, ta hanyoyi daban daban. Inda ta taimaki nahiyar Afirka sosai a kokarinta na dakile cutar COVID-19, gami da samun yabo sosai daga kasashen na Afirka.

Bisa da la’akari da yadda cutar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa sosai a nahiyar Afirka, yayin ziyarar ministan Sin a kasashen Afirka, kasar Sin ta nuna cewa, za ta ci gaba da samarwa kasashen Afirka da kayayyakin da suke bukata, da tura tawagogin kwararrun likitoci zuwa wasu kasashen Afirka da suka tura musu kwararru, da gaggauta gina hedkwatar cibiyar hana yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka, da hadin gwiwa da wasu kasashen dake nahiyar Afirka, wadanda suke bukatar samun allurar rigakafin cutar COVID-19, da taimakawa kasashen Afirka samun allurar rigakafin cutar COVID-19 masu inganci da rahusa, da dai sauransu.

A jiya Lahadi, an kaddamar da aikin shigar da allurar rigakafin cutar COVID-19 kasar Seychelles, inda shugaban kasar Wavel Ramkalawan ya zama mutum na farko na kasar da aka yi masa allurar rigakafin da kamfanin kasar Sin SINOPHARM ya samar. Hakan ya shaida cikakken imani da zumunta da ake samu tsakanin bangarorin Sin da Afirka, wanda ya kara karyata jita-jitar da wasu kasashen yammacin duniya suke yadawa, wai “kasar Sin na neman Kara yin tasiri a nahiyar Afirka bisa yin amfani da cutar COVID-19”.

Yanzu haka kasashen Afirka na fuskantar kalubaloli na yaduwar annoba, da tabarbarewar tattalin arziki. Ganin haka ya sa kasar Sin, a matsayinta na aminiyar kasashen Afirka ta gaske, daukar niyyar taimakawa kasashen Afirka farfado da tattalin arzikinsu. Don haka a bangare guda, kasar Sin ta kan yi magana a madadin kasashen Afirka, inda ta yi hadin gwiwa tare da mambobin kunigyar G20 wajen aiwatar da shawarar dakatar da bashin da ake bin kasashen Afirka. Sa’an nan a wani bangare na daban, kasar Sin na kara kokarin mu’amala da kasashen Afirka, don neman farfado da wasu manyan ayyukan da ake gudanar wa a kasashen Afirka, da kara saurin aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, don taimakawa kasashen Afirka daidaita tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a.

Wani abun lura shi ne, a yayin wannan ziyarar da minista Wang ya yi, kasar Sin ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa karkashin laimar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” tare da Congo Kinshasa, da Botswana. Lamarin da ya sanya yawan kasashen dake nahiyar Afirka da suka shiga tsarin zuwa 46.

A kwanan baya, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, “Idan har kasa tana fuskantar matsalar rashin kayayyakin more rayuwa, to, ba za ta samu damar samun ci gaba mai dorewa ba. Don haka, muna godiya ga kasar Sin kan yadda take taimaka mana raya kayayyakin more rayuwa, da suka hada da layin dogo, da hanyar mota, da kayayyakin da suka shafi wutar lantarki da tsaro, da makamantansu. “Lale shugaban ya fadi abin da cikin zukatan sauran kasashen dake nahiyar Afirka.

Wane ne abokin nahiyar Afirka na gaskiya? Amsar a bayyana ta ke. Bayan da aka gabatar da wasu matakai 8 na karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a taron dandalin hadin kan Sin da Afirka FOCAC na shekarar 2018, ya zuwa yanzu an riga an kammala kasha 70% na dukkan ayyukan da aka yi shirin gudanar da su. Sa’an nan a sabuwar shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin inganta hadin kai da kasashen Afirka, don kafa wata al’umma mai kayakkyawar makoma ta bai daya tsakanin sassan biyu. (Bello Wang)

Bello