logo

HAUSA

Gudanawar Dokar Kare Hakkin Al’umma Yana bada Gudummawar Aiwatar Da Harkokin Kasa Bisa Dokoki A Dukkanin Fannoni

2021-01-10 19:22:05 CRI

Gudanawar Dokar Kare Hakkin Al’umma Yana bada Gudummawar Aiwatar Da Harkokin Kasa Bisa Dokoki A Dukkanin Fannoni_fororder_210110-sharhi-maryam-hoto

Daga ranar 1 ga watan Janairun bana, an fara gudanar da dokar kare hakkin al’umma ta Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin. Wannan shi ne babban matakin da aka taka wajen inganta tsarin gudanarwar harkokin kasa cikin sabon zamani, kuma, babban sakamakon da aka samu wajen karfafa aikin doka bisa tsarin gurguzu a wannan sabon zamani da muke ciki.

Kamar yadda Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, gudanar da dokar kare hakkin al’umma yadda ya kamata, zai tabbatar da kare hakkin al’umma bisa dokoki yadda ya kamata, ta yadda, zai daidaita mu’amalar dake tsakanin al’umma a fannoni da dama, da kuma kiyaye zaman lumana na kasar. Dokar kare hakkin al’umma, doka ce dake tabbatar da ci gaban kasa cikin dogon lokaci mai zuwa, kuma dokar dake kare hakkin dukkanin jama’ar kasa, za ta taka muhimmiyar rawa a fannin tallafawa al’umma, yayin da zata ba da gudummawa wajen gina wata kasa ta zamani daga dukkanin fannoni.

Kafin gudanarwar dokar kare hakkin al’ummar, kasar Sin tana da ka’idojin kare hakkin al’ummarta, da doka kan ikon mallakar dukiya, da dokar kwangila da sauran dokokin dake shafar harkokin al’umma da kasuwanci. Wadannan dokoki sun ba da gudummawa wajen raya tattalin arziki da zaman takewar al’umma cikin dogon lokacin da ya gabata. Amma, sabo da ci gaban bunkasuwar kasar Sin, wadannan dokokin sun kasa biyan bukatun al’umma ta fuskar harkokin doka. Shi ya sa, gudanawar dokar kare hakkin al’umma ya dace da moriya da fatan al’umma, da kuma bunkasuwar zamantakewar al’umma.

Gabatar da dokar ya karfafa ra’ayin al’umma game da kare hakkinsu bisa doka, da kuma gudanar da harkokin kasa bisa doka, tabbas ne, zai inganta ayyukan gudanarwar harkokin kasa bisa dokoki a dukkanin fannoni cikin wannan sabon zamanin da muke ciki. (Maryam Yang)