logo

HAUSA

Ziyarar Wang Yi a Afirka za ta zurfafa hulda tsakanin Sin da Afirka bayan ganin bayan COVID-19

2021-01-09 16:15:57 CRI

Ziyarar Wang Yi a Afirka za ta zurfafa hulda tsakanin Sin da Afirka bayan ganin bayan COVID-19_fororder_1

Ziyarar dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan wajen kasar Wang Yi zuwa Afirka, ita ce ta farko da duk wani ministan wajen Sin ke kaiwa ketare a duk farkon ko wace shekara, cikin shekaru 31 a jere, tun daga shekarar 1991. Hakan na nuni ga irin yadda Sin da kasashen Afirka, ke ji da junan su, a fannin kawance da kuma tunkarar wahalhalu tare.

Hakika tun bayan da aka gamu da matsalar yaduwar cutar COVID-19 a fadin duniya, kasar Sin da kasashen Afirka suna hada kai domin ganin bayan annobar, ziyarar da Wang Yi ya yi a kasashen Afirka ta nuna sahihiyar fata da niyya mai karfi na gwamnatin kasar Sin wajen kara zurfafa huldar dake tsakanin sassan biyu bayan ganin bayan annobar cutar numfashi ta COVID-19.

A shekarar 2020 da ta kare, kasar Sin da kasashen Afirka sun yi kokari matuka domin taimakawa juna da kuma goyon bayan juna, ta yadda za su gina kyakkyawar makoma ta bai daya ta Sin da Afirka.

An lura cewa, tun barkewar annobar COVID-19, ba ma kawai kasar Sin ta taka rawar gani wajen ba da tallafi ga kasashen Afirka ba, har ma ta kasance kasa daya kacal wadda ta kira taron kolin musamman da kasashen Afirka domin tattauna yadda suke gudanar da hadin gwiwa kan aikin dakile annobar. Yanzu haka, sassan biyu sun riga sun samu sakamako, wato kasar Sin ta yi nasarar hana yaduwar cutar a kasar, kuma adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ko adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar a nahiyar Afirka bai kai hasashen da wasu hukumomin kasa da kasa suka yi ba.

Ban da haka, minista Wang Yi ya taba bayyana cewa, za a shirya sabon taron dandalin tattaunawar kasar Sin da kasashen Afirka a Senegal a bana, inda kasar Sin take son kara habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka a bangarorin samar da allurar rigakafin cutar COVID-19, da farfadowar tattalin arziki, da kuma raya kasa ta hanyar sauya salon bunkasuwa, ta yadda za a amfanawa al’ummun sassan biyu tare kuma da gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka.

Domin cimma burin, ya dace sassan biyu su kara kokari saboda annobar COVID-19 ta kawo illa ga hadin gwiwar tattalin arzikinsu, amma fifikon Sin a bangarorin fasahohin zamani da jari da fasahohin raya kasa, da fifikon kasashen Afirka a bangarorin kasuwa, da albarkatan halittu, da kuma boyayen karfi za su dogara da juna yayin da suke gudanar da hadin gwiwa, kana bayan ganin annobar, tsarin jigilar kayayyaki da tsarin samar da kayayyaki za su farfado, lamarin da zai kai hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu zuwa sabon matsayi gaba. Ana iya cewa, ziyarar Wang Yi a Afirka a farkon sabuwar shekarar za ta kara zurfafa hulda tsakanin sassan biyu bayan ganin bayan annobar. (Jamila)

jamila