logo

HAUSA

Yaya za a kai ga fita daga kangin talauci a yayin da ake fuskantar annobar COVID-19?

2021-01-08 16:03:07 CRI

Yaya za a kai ga fita daga kangin talauci a yayin da ake fuskantar annobar COVID-19?_fororder_1

Kauyen Jinmi da ke lardin Shaanxi na arewacin kasar Sin kauye ne da a baya aka san shi da talauci. Sai dai yanayin yankin da kauye ke ciki ya dace ne da noman nau’in laimar kwado da ake amfani da shi a fannin abinci, da kuma magunguna. A cikin ‘yan shekarun baya kuma, mazauna kauyen sun yi kokarin bunkasa aikin noman nau’in laimar kwado, da aikin harhada magungunan gargajiya, da kuma harkokin yawon shakatawa, lamarin da ya sa rayuwarsu ta inganta sosai.

Yaya za a kai ga fita daga kangin talauci a yayin da ake fuskantar annobar COVID-19?_fororder_2

Sai dai annobar COVID-19 da ta barke ba zato a farkon shekarar 2020, ta kawo babbar matsala ga manoman kauyen wajen sayar da amfanin gonarsu, laimar kwadi sun taru a kauyen a sakamakon yadda aka kasa sayar da su. Amma ta kafofin yanar gizo, manoman sun samu damar ci gaba da sayar da laimar kwadon zuwa sassa daban daban na kasar.

Yaya za a kai ga fita daga kangin talauci a yayin da ake fuskantar annobar COVID-19?_fororder_4

A watan Afrilun shekarar 2020, an samu wani babban bako a kauyen, wato shugaban kasar Sin Xi Jinping. Kuma hoton bidiyo game da yadda shugaban ya nuna yabo ga dandalin sayar da kayayyaki ta yanar gizo na kauyen, ya samu farin jini a kafofin yanar gizo, lamarin da ya sa mutane miliyan 20 suka sayi laimar kwadon daga kafar wannan dandali nan da nan, kuma manoman kauyen sun sayar da laimar kwadon da nauyinsu ya kai ton 24 gaba daya, don haka masu ziyartar shafukan yanar gizo na kasar Sin suke kiran shugaba Xi Jinping, mai tallata kaya mafi kwarewa na kasar.

Yaya za a kai ga fita daga kangin talauci a yayin da ake fuskantar annobar COVID-19?_fororder_5

A farkon watanni 9 na shekarar 2020, kudin da mazauna kauyukan kasar Sin suka samu wajen sayar da hajoji ta yanar gizo ya kai triliyan 1.2,adadin da ya karu da kaso 7.8% bisa na makamancin lokacin bara. A watan Nuwamban shekarar 2020, an fitar da dukkanin gundumomi masu fama da talauci 832 na kasar daga kangin da suke ciki, lamarin da ya alamanta yadda kasar ta cimma burinta na saukaka fatara, duk da munanan matsalolin da annobar COVID-19 ta haifar mata.

Yaya za a kai ga fita daga kangin talauci a yayin da ake fuskantar annobar COVID-19?_fororder_6

A game da haka, Madam Gertrude Trudi Makhaya, mai ba da shawara ga shugaban kasar Afirka ta kudu kan harkokin tattalin arziki ta bayyana cewa, “hakan ya nuna mana cewa, za a cimma babbar nasara, idan dai an dauki al’umma da muhimmanci.”