logo

HAUSA

Kasar Sin na kara janyo hankalin ‘yan kasar da suka yi karatu a ketare

2021-01-08 14:27:46 CRI

Kididigar da ma’aikatar ilimi ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa daliban kasar da suka yi karatu a ketare sun kara nuna sha’awar dawowa gida, bayan kammala karatu. Sai dai mene ne dalilin da ya sa suke zabar dawowa gida, maimakon ci gaba da zama a kasashen waje?

Huang Yuanhao, wani dan kasar Sin ne, wanda ya taba kwashe fiye da shekaru 10 yana karatu a kasashen Amurka da Canada, don nazarin fasahar auna tazara ta haske. Bayan da ya kammala karatunsa, ya dawo kasar Sin, inda ya bude wani kamfani na kansa, sa’an nan ya gayyaci abokansa da dama, wadanda suka taba karatu a wasu sanannun jami’o’in kasashen waje, don su yi aiki a kamfaninsa. A cewar Huang,

“Mun yi shekaru fiye da 10 muna nazarin wasu fasahohi tare. Kuma muna fatan yin amfani da fasahohinmu wajen samar da wasu kayayyaki, da taimakawa karin kamfanonin kasar Sin takara a kasuwannin kasa da kasa.”

Alkaluman da ma’aikatar ilimi ta kasar Sin ta gabatar, sun nuna cewa, tsakanin shekarar 2016 zuwa ta 2019, daliban kasar Sin miliyan 2 da dubu 518 sun tafi karatu kasashen waje, yayin da wasu dalibai miliyan 2 da dubu 13 suka dawo kasar Sin bayan gama karatu a ketare. Wato kimanin kashi 80% na daliban sun dawo kasarsu, don raya sana’o’insu. Kana a shekarar 2020 da ta gabata, an ci gaba da samun karuwar daliban da suke dawowa gida. Cheng Jiacai, shi ne darektan cibiyar samar da hidima ga dalibai masu karatu a kasashen waje karkashin ma’aikatar ilimi ta kasar Sin, ya ce,

“Idan mun dubi alkaluman da aka samar a cibiyarmu, za mu gano cewa, a shekarar 2020, kimanin fiye da mutane dubu 300 sun nemi dawowa gida. Adadin da ya karu da dubu 30, idan an kwatanta da na shekarar 2019.”

Wani kamfanin dake taimakawa mutane samun guraben aiki na kasar Sin, ya ce, daga watan Nuwamban shekarar 2019 zuwa watan Afrilun shekarar 2020, kamfanin ya samar da hidima ga karin mutanen da suka taba karatu a kasashen waje, inda yawan karuwar ya kai kashi 213%. Kana an fi samun kaurwar a shekarar 2020. A wajen wani bikin samar da guraben aikin yi ga daliban da suka gama karatu a kasashen waje, da ya gudana a birnin Shanghai na kasar Sin, a kwanan baya, mutane da yawa sun nuna fatansu na samun aikin yi a kasar Sin, bisa la’akari da yanayin ci gaba da aka samu a kasar, a bangaren shawo kan yaduwar cutar COVID-19, da raya tattalin arziki. Inda suka bayyana kamar haka:

“Na dawo daga kasar Birtaniya. A nan gida an fi samun manyan kamfanoni. Burina shi ne samun damar aiki a wani babban kamfani, don neman samun karin kwarewar aiki.”

“Karatun da muka yi a kasashen waje ya sa mu samun karin ilimi sosai. Sa’an nan idan aka yi la’akari da damar raya kanmu, zama a gida zai fi zama a ketare.”

Ban da wannan kuma, Chu Chaohui, wani masani na cibiyar nazarin aikin koyarwa ta kasar Sin, ya ce, dalilin da ya sa wadannan daliban da suka yi karatu a kasashen waje suke kokarin neman ayyuka a gida, shi ne, a wani bangaren, ana fuskantar mawuyacin hali a fannin neman ayyukan yi a kasashen waje, yayin da a bangare na daban kuma, tattalin arzikin kasar Sin na kyautatuwa sosai. Chu ya ce,

“Da farko dai yanayin da ake ciki na neman ayyukan yi a kasashe daban daban ya sauya sosai. Yanzu dalibai su kan sha wahala sosai, idan suna son samun aikin yi a kasar da suka yi karatu, ko kuma a sauran kasashe. Ban da wannan kuma, wasu daliban da suka riga suka samu aikin yi a kasashen waje, suna neman samun wurin da za su iya raya harkokinsu bisa ra’ayinsu. Sa’an nan saboda a nan gida ana samar musu da wadannan damammaki, shi ya sa suka zabi dawowa gida. ”

A cewar Chu, wadannan daliban da suka dawo gida, za su taimakawa kasar Sin cika burinta na kirkiro karin sabbin fasahohi don raya tattalin arzikinta. (Bello Wang)

Bello