logo

HAUSA

Ko akwai yiyuwar Amurka a yanzu ta fi Amurkan kafin shekaru 4 tsaro?

2021-01-08 19:32:28 CRI

A jiya Alhamis mujallar “Time” ta Amurka, ta wallafa wani hoto game da boren da aka yi a birnin Washington, wato yadda ‘yan daba suka kutsa kai a cikin ginin majalisar dokokin kasar, inda aka bayyana cewa, an lalace demokuradiya. Mai tsara fasalin kayan sawa a New York Kenneth Cole ya bayyana cewa, hoton ya nuna ranar da ta gabata a kasar Amurka, da kuma shekaru hudu da suka gabata a kasar.

A ranar 6 ga wata kuwa, jaridar “Washington Post” ta wallafa wani rahoto mai taken “Pompeo wanda ya saba da yin karya, yana kokarin gyara tarihin Amurka na shekaru hudu da suka wuce”, inda aka bayyana cewa, Pompeo ya fara yin karya tun daga ranar farko ta sabuwar shekarar nan ta 2021. Inda a ranar ya bayyana cewa, Amurka a yanzu ta fi Amurkan kafin shekaru hudu tsaro.

Amma fa shaidu na gaske sun nuna yanayin da Amurka ke ciki yanzu.

Ga misali, a halin yanzu, annobar COVID-19 tana ci gaba da bazuwa cikin sauri a kasar, har ta kai adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya riga ya kai sama da dubu 370. Kuma abun bakin ciki shi ne, an yi hasashen cewa, a cikin wata guda mai zuwa, adadin mutanen da za su iya mutuwa sakamakon cutar zai kai dubu 115, kuma abun damuwa shi ne, hargitsi tsakanin al’ummun kasar kan faru a fadin kasar.

Hakika boren da ya faru a ranar 6 ga wata, ya sake shaida cewa, Amurka tana fuskantar rikicin siyasa, ba wai batu ne na nuna rashin jin dadi kan sakamakon babban zaben kasar kawai ba.

A bayyane take cewa, demokuradiya da ‘yancin kai da ‘yan siyasar Amurka suke yadawa, ba su haifar da demokuradiya da ‘yancin kai ga al’ummun kasar ba. Kuma tsokacin Pompeo cewa wai Amurka a yanzu ta fi Amurka kafin shekaru 4 da suka gabata, karya ce kawai. (Jamila)