logo

HAUSA

Gurgunta kamfanonin Sin ya nuna mugun yunkurin ‘yan siyasar Amurka

2021-01-08 19:26:46 CRI

Gurgunta kamfanonin Sin ya nuna mugun yunkurin ‘yan siyasar Amurka_fororder_1

A kwanakin baya bayan nan, shugaban kasar Amurka ya sa hannu kan umurnin hana cinikkayar manhajojin wayar salula guda 8 na kasar Sin, bisa fakewa da tsaron kasa, ciki har da manhajojin biyan kudi ta Alipay da WeChat, wannan mataki ne na daban, na gurgunta kamfanonin kasar Sin da ‘yan siyasar Amurka suka dauka, ta hanyar yin amfani da karfin kasa.

A cikin shekaru hudu da suka gabata, ‘yan siyasar Amurka suna mayar da kasar Sin ‘yar takara mafi girma ta kasarsu, a don haka sun dauki matakan sanya takunkumi iri daban daban kan kamfanonin kasar Sin, musamman ma kamfanonin kimiyya da fasahar zamani, domin hana ci gaban kasar Sin.

Alal misali, hana kamfanin Huawei wanda ke da rinjaye a bangaren fasahar 5G, ya gudanar da cinikayya a kasar, ko kuma ba da umurni ga dandalin sada zumunta na TikTok, ya sayar da harkokinsa a kasar. Yanzu haka sun matsa lamba ga kasuwar hada-hadar kudi ta New York, da lallai sai ta fitar da manyan kamfanonin sadarwa uku na kasar Sin daga kasuwar ta, kuma gwamnatin Amurka ta dauki matakan ne bisa fakewa da tsaron kasa, ba tare da nuna wasu shaidu na hakika ba ko kadan.

Gurgunta kamfanonin Sin ya nuna mugun yunkurin ‘yan siyasar Amurka_fororder_2

Kamar yadda wasu masu lura da al’amuran yau da kullum suka bayyana, matakan da gwamnatin Amurka ta dauka sun nuna mugun yunkurinta.

Da farko, wasu ‘yan siyasar Amurka wadanda ke yin adawa da kasar Sin, suna shafawa kasar Sin bakin fenti ta hanyar gurgunta moriyar kamfanonin kasar, ta yadda za su cimma burin baza bayanan karya game da kasar Sin ga al’ummun su.

Na biyu, wasu ‘yan siyasar kasar, da fitattun ‘yan kasuwan kasar, suna fatan za su hana ci gaban kamfanonin kasar Sin, ta hanyar kayyade harkokinsu. Ban da haka kuma, wasu masu tsattsauran ra’ayi na kasar, suna son hana hadin gwiwar tattalin arzikin dake tsakanin kasar Sin da Amurka, ta hanyar daukar matakin gurgunta kamfanonin kasar Sin.

Kwanaki kusan 10 kacal suka rage ga gwamnati mai ci ta Amurka, don haka ya dace ta gyara kuskuren ta a kan lokaci, saboda a ko da yaushe, kasar Sin tana nacewa manufar kiyaye ikon mulki, da tsaro, da kuma kwanciyar hankalinta. (Jamila)