logo

HAUSA

A karon farko cikin sama da shekaru 100 ‘yan daba sun kutsa kai cikin zauren majalissar dokokin Amurka

2021-01-07 20:03:22 CRI

A karon farko cikin sama da shekaru 100 ‘yan daba sun kutsa kai cikin zauren majalissar dokokin Amurka_fororder_1

Idan a ce wannan wuri ba ya dauke da tutar Amurka, shin za mu iya yarda cewa zauren majalissar dokokin Amurka ne a jiya Laraba 6 ga watan Janairun nan?

Wannan mutumin magoyin bayan shugaba Trump ne, shugaban Amurka na 45. Yana zaune kan kujerar kakakin majalissar wakilan kasar Nancy Pelosi, inda ya dora kafarsa kan teburin dake gaban kujerar. A wajen ofishin kuwa, cuncurundon jama’a ne ke ci gaba da yamutsi.

Magoya bayan Trump da ‘yan sanda sun yi tawo mu gama a zauren majalissar dokokin. Yayin da mataimakin shugaban kasar Mike Pence ke jagorantar zaman majalissar. Lokacin da kuma ‘yan majalissar ke kidayar kuri’un wakilan masu zaben shugaban kasa da aka kada a shekarar 2020 da ta kare. A gabar da aka kai kidayar kuri’u 538, masu boren sun riga sun ci karfin masu tsaron majalissar, don haka ala tilas ‘yan majalissar suka fice daga zaman da suke yi cikin gaggawa. Yayin da wasu daga ‘yan majalissar da ba su fice da wuri ba, suka boya karkashin kujerun zauren.

Wannan dai hargitsi ya haifar da dauki ba dadi, inda aka harbe mutane 4.

An dai rika kiran wadannan mutane da suka yi kutse cikin zauren da ‘yan daba, Amma dukkanin su Amurkawa ne, ba wani bako ‘dan wata kasa ta waje.

A baya, dakarun Birtaniya sun taba mamaye birnin Washington a shekarar 1814, inda suka kone ginin White House, da zauren majalissun dokokin kasar na Capitol Hill. A wannan karo kuwa, ran 6 ga watan Janairun nan, ‘yan kasar Amurka ne da kan su suka yiwa ginin na Capitol Hill kutse, wanda hakan ya zama irin sa na farko a tarihin kasar.

Shugaba Trump ya ki ya amsa shan kaye a babban zaben kasar da ya gudana, kana magoya bayan sa kuma, sun maida martani ta hanyar tayar da tarzoma.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya nuna damuwar sa. Yana mai cewa wannan abun kunya ne. Ya kamata Amurka ta kasance abar koyi wajen kare dimokaradiyya. Kuma abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne, mika mulki cikin lumana kuma bisa tsari.

Idan da za a ce ga misali, bayan gudanar da wani zabe, a samu kin amincewa da sakamakon, kuma a samu irin wannan tarzoma, da tashin tashina, kuma a ce a wata kasa ce dake nahiyar Asiya, ko Gabas ta Tsakiya ko Afirka. Shin ko wace irin kalma kafofin watsa labaran yammaci za su yi amfani da ita wajen kwatanta wannan al’amari?

Kana wace sanarwa shugaban Amurka zai fitar, me mataimakin shugaban kasar da ‘yan majalissar dokokin Amurka za su ce game da hakan?

Kila a ga kalamai irin su “Take dimokaradiyya”, da "tozarta hakkin bil Adama" da "Dole a kawar da danniya" suna ta fita daga kafofin watsa labaran.

Tsawon shekaru, mun saba jin irin wadannan kalamai cikin bayanan da Amurka ke fitarwa.

A karon farko cikin sama da shekaru 100 ‘yan daba sun kutsa kai cikin zauren majalissar dokokin Amurka_fororder_2

Sai dai kuma kash, a yau, wadannan kalmomi ne da ake amfani da su kan Amurkan. Wannan kasa mai rajin kare dimokaradiyya a duniyar yau, wadda ke rike da ragamar “Kasa mafi karfi” a fannoni da dama, ciki har da na tattalin arziki, kimiyya da fasaha, tana yiwa kan ta kallo wadda ta wayar da kan bil Adama.

Zababben shugaban Amurka Joe Biden, shi kan sa ya kira masu zanga zangar da “‘yan daba”, yana mai kiran wadanda suka kutsa cikin ginin Capitol da sunan masu "Tada tarzoma." A hannu guda kuwa, shugaba Trump ya yi kira gare su, da su "kai zuciya nesa", amma duk da hakan ya ci gaba da cewa, an yi masa kwacen zaben da ya lashe.

A shekarar 1863, shugaban Amurka na 16 a wancan lokaci Abraham Lincoln, wanda shi ne ya zartas da dokar hana cinikin bayi, ya gabatar da wani jawabi da ya yi fice, wanda aka yiwa lakabi da “Jawabin Gettysburg”, inda cikin sa yake cewa, “Dole mu tsarkake kasar mu karkashin albarkar da ubangiji ya yi mata, kuma gwamnati ta zama mallakin jama’a, gwamnatin al’umma da jama’a za su ji dadin ta, wadda kuma za ta wanzu har abada”.

A yau, wadannan “yan daba” sun yi abun da suka ga dama yayin da majalissar dokokin kasar su ke gudanar da taro, kuma shugaban da ya sha kaye ya ki amincewa ya amshi sakamakon da aka fitar karkashin “Zaben dimokaradiyya”. Wadannan al’amura sun mayar da kalaman da shugaba Lincoln ya taba yi, tamkar wata tatsuniya kawai. (Saminu)