logo

HAUSA

Yadda ‘yan siyasar Amurka za su daidaita boren kasar?

2021-01-07 18:54:59 CRI

Yadda ‘yan siyasar Amurka za su daidaita boren kasar?_fororder_1

Bisa tsarin babban zaben kasar Amurka, jiya Laraba ranar 6 ga watan Janairu, rana ce da majalissun dokokin kasar biyu ke aikin tabbatar da sakamakon babban zaben kasar. Sai dai kuma a wannan rana, an samu barkewar zanga-zanga a birnin Washington, inda masu goyon bayan shugaban kasar mai ci, suka kutsa kai a cikin ginin majalisar dokokin kasar, wanda ke matsayin koli, a ikon kafa dokar kasar.

Makasudinsu shi ne dakatar da kidayar kuri’un wakilan masu zabe da majalissar ke gudanarwa, inda kawo yanzu boren ya riga haifar da mutuwar mutane hudu, kana mutane da dama suka ji raunuka.

Hakika daukacin kasashen duniya sun kadu, da aukuwar boren da ya faru a kasar Amurka, wadda take kiran kanta “kasa mai ‘yancin kai da demokuradiya”, saboda ‘yan siyasar Amurkan sun fi son tayar da hankali a sauran kasashe.

Alal misali, masu tayar da hankali, sun taba kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, a watan Yunin shekarar 2019, inda suka yi barna mai tsanani, amma a wancan lokaci ‘yan siyasar Amurka, sun kira lamarin “abu mai kyan ganin da ake kallo”, kuma suna bayyana cewa, masu tarzoma suna kare demokuradiya ne, sai dai a yanzu haka da boren ya faru ne a cikin kasarsu, ‘yan siyasar Amurka sun mayar da shi “boren siyasa”, har suna bukatar a hukunta masu tayar da tarzoma bisa doka.

Al’ummun kasa da kasa, sun sake ganin ma’auni iri biyu da Amurka take amfani da shi, inda ‘yan siyasar Amurka ke daukar matakai bisa fakewa da demokuradiya a lokacin da suka ga dama, ko shakka ba bu, ana iya cewa, ‘yan siyasar Amurka suna keta demokuradiya.

Ga shi dai game da babban zaben kasar, har yanzu shugaban kasar mai ci ya ki yarda da sakamakon da aka samu ta hanyar demokuradiya. To amma shin ko ta yaya ‘yan siyasar Amurkan za su daidaita boren da ya faru, dake jawo hankalin al’ummun kasa da kasa? Ana sa ran za su daidaita matsalar yadda ya kamata, kana su kauracewa sake yada salon demokuradiyar Amurka mai fuska biyu, saboda wannan salo ya riga ya kasance abun dariya. (Jamila)