logo

HAUSA

Ghana ta yi sufurin kayanta na farko karkashin AfCFTA

2021-01-06 10:51:02 CRI

Ragotanni daga kasar Ghana na cewa, kasar ta yi sufurin hajojinta na farko karkashin yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka (AfCFTA).

A ranar Litinin ne dai, Kamfanin Kasapreko dake samar da kayayyakin da suka shafi barasa da na Ghanadour Comsetis dake samar da kayayyakin kwalliya, su ka fitar da hajojinsu ta jiragen sama da na ruwa bi da bi zuwa kasashen dake nahiyar.

Da yake Karin haske kan wannan batu, darektan raya harkokin cinikayyar kasa da kasa na kamfanin Kasapreko, Francis Holly Adza, ya ce, “muna matukar farin ciki da wannan yarjejeniya, da ma kasancewa daya daga kamfanonin farko, da za su fitar da hajojinsu daga Ghana karkashin wannan yarjejeniya”

Ya ce, ya zuwa yanzu, kamfanin ya riga ya fitar da kayayyakinsa zuwa kasashe 14 na Afirka, zai kuma yi amfani da damar dake cikin wannan yarjejeniya, wajen kara fafada kasuwarsa zuwa ragowar sassan nahiyar.

Shi ma ministan cinikayya da masana’antu na kasar Ghana Alan Kyerenmateng, cewa ya yi, idan har ana fatan yarjejeniyar ta kai ga samun nasara, wajibi ne a baiwa kanana da matsakaitan masana’antu damar taka muhimmiyar rawa wajen aiwatarwa da ita yadda ya kamata.(Ibrahim)